Rikicin, wanda ya dauki kusan awa daya ana yi, jami’an tsaro ne suka shawo kan lamarin da karfe 9.30 na dare haka kuma an jikkata mutum tara. / Hoto: Deby

Akalla ‘yan bindiga 18 ne suka mutu sannan aka kashe ma'aikacin gwamnatin Chadi ɗaya a lokacin da 'yan bindiga suka yi yunkurin kutsawa cikin fadar shugaban kasar da ke N'Djamena babban birnin kasar Chadi a ranar Laraba, kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka bayyana.

An kai harin ne a unguwar Djambal Bahr da ke birnin N'Djamena inda aka yi artabu tsakanin masu gadin fadar da 'yan bindigar.

Rikicin, wanda ya dauki kusan awa daya ana yi, jami’an tsaro ne suka shawo kan lamarin da karfe 9.30 na dare haka kuma an jikkata mutum tara.

Kawo yanzu dai ba a bayyana sunayen maharan ba, yayin da wasu majiyoyi ke hasashen cewa kungiyar ta'addanci ta Boko Haram ce ta kai harin, amma babu wani tabbaci daga jami'ai.

Gwamnatin Chadi ta bayyana harin a matsayin "yunkurin juyin mulki."

Ba a bayyana inda shugaba Mahamat Idriss Deby Itno yake a lokacin harin ba.

Wasu bidiyoyi da ke yawo a shafukan sada zumunta sun nuna maharan sanye da kayan farar hula.

AA