Rahoton bai bayar da wani karin bayani ba kuma ministan yada labarai Michael Makuei bai amsa bukatar jin ta bakinsa ba. / Hoto: Reuters

Wani jirgin sama ɗauke da fasinjoji 21 da ma'aikatansa a jihar Unity ta Sudan ta Kudu ya yi haɗari a ranar Laraba, inda mutum 18 suka rasu, kamar yadda gidan rediyon Majalisar Dinkin Duniya ya ruwaito.

Jirgin dai ya taso ne daga wani wurin haƙar ɗanyen mai da ke arewacin ƙasar inda ya faɗi bayan ya tashi, kamar yadda gidan rediyon Miraya ya tabbatar wanda ke ƙarƙashin kulawar jami’an wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya a Sudan ta Kudu.

Rahoton bai bayar da wani karin bayani ba kuma ministan yada labarai Michael Makuei bai amsa bukatar jin ta bakinsa ba.

Hatsarin jiragen sama da dama sun faru a Sudan ta Kudu da ke fama da yaki a cikin 'yan shekarun nan. A watan Satumban 2018, aƙalla mutum 19 ne suka mutu a lokacin da wani karamin jirgin sama ɗauke da fasinjoji daga Juba babban birnin kasar zuwa birnin Yirol ya yi hatsari.

A shekarar 2015, mutane da dama ne suka mutu a lokacin da wani jirgin dakon kaya da kasar Rasha ta ƙera tare da fasinjoji ya yi hatsari bayan tashinsa daga filin jirgin saman Juba babban birnin kasar.

Reuters