Kwamishinan lafiya na Kano Dr, Abubakar Labaran Yusuf ya ce wuar ta yi wa mutanen illa, domin fiye da rabin jiki waɗanda aka kai asibiti ya ƙone.  / Hoto: Kano Police

Rundunar 'ayn sanda jihar Kano a arewacin Nijeriya ta ce mutum 11 daga cikin mutanen da aka cinna wa wuta a wani masallaci sun mutu, yayin da sauran suke samun kulawa a asibiti.

Sai dai tun da fari a ranar Alhamis, Kwamishinan Lafiya na Kano Dokta Abubakar Labaran Yusuf ya shaida wa TRT Afirka Hausa cewa “zuwa karfe 1:30 na ranar Alhamis da na bincika, mutum tara ne suka mutu daga cikin waɗanda aka kawo mana asibiti.”

Daga baya ne mutum biyu suka sake rasuwa kamar yadda rundunar 'yan sandan ta tabbatar wa TRT Afrika Hausa.

Dokta Abubakar ya ce sauran mutanen 14 kuma suna nan suna karɓar magani. Kwamishinan ya ce tun lokacin da aka kawo mutanen likitoci sun fahimci wutar ta yi musu mummunar illa, “dukkansu fiye da rabin jikinsu ya ƙone.”

“Kuma gaskiya babban haɗari ne ga ɗan'adam ya samu irin wannan ƙunar.” Ya ce hakan ce ma ta sa aka tattaro duk wani ƙwararren likita da ya shafi ƙuna, domin bai wa mutane kulawa ta musamman.

Kwamishinan na lafiya ya ƙara da cewa a yanzu haka an yi wa sauran mutanen 14 duk abin da ya kamata, kuma ana ba su duk kulawar da ta dace, duba da irin illar da wutar ta yi musu.

A ranar Laraba ne wani matashi ya watsa wa mutane man fetur sannan ya kunna musu wuta, a lokacin da suke Sallar Asuba a wani masallaci a ƙauyen Gadan da ke Larabar Abasawa a Ƙaramar Hukumar Gezawa, kamar yadda rundunar ‘yan sandan Kano ta sanar.

Sanarwar ‘yan sandan ta ce bincike ya nuna cewa wanda ake zargi Shafi’u Abubakar ya ƙona masallatan ne saboda matsalar da ya samu da ‘yan'uwansa kan batun rabon gado.

Wasu bayanai sun ce da dama daga waɗanda ibtila’in ya afka wa ‘yan'uwan mutumin ne da suke da matsalar ta rabon gado.

Wasu jaridun Nijeriya sun rawaito cewa Shafi’u ya kulle masallacin ne lokacin da ya kunna wutar, abin da ya sa kenan mutane da dama suka jikkata kafin a kawo musu ɗauki.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce tuni ta kama wanda ake zargi da cinna wuta a matsallacin.

Kakakin rundunar Abdullahi Haruna Kiyawa ya shaida wa TRT Afrika Hausa cewa za su gurfanar da wanda ake zargi a kotu da zarar sun kammala bincike.

TRT Afrika da abokan hulda