Wata gagarumar gobara ta tashi a babbar ma'ajiyar makamai ta sojojin Chadi da ke N'Djamena, babban birnin ƙasar, kamar yadda gwamnati ta tabbatar ko da yake ba ta yi cikakken bayani kan abin da ya haddasa gobarar ba.
An ji ƙarar abubuwa suna fashewa a ma'ajiyar makamai da ke yankin Goudji a kusa da filin jirgin saman ƙasar ranar Talata, in ji wani wakilin kamfanin dillancin labarai na AFP, inda ya ƙara da cewa makamai sun riƙa yin rimi suna fashewa a sararin samaniya kuma yankin ya turniƙe da baƙi da jan hayaƙi.
Mazauna yankuna da ke da nisa da wurin sun ji ƙarar fashewar makaman. Kazalika an ci gaba da jin ƙarar awa ɗaya da rabi bayan fashewar farko.
Daga bisani Shugaba Mahamat Idriss Deby Itno ya tabbatar da mutuwar mutane sakamakon lamarin, sannan ya yi ta'aziyya ga iyalan waɗanda suka rasu. Amma bai faɗi adadin mutanen da suka mutu ba.
Ministan Harkokin Waje Abderaman Koulamallah, wanda kuma shi ne kakakin gwamnati, ya sanar a shafin Facebook cewa an samu "gagarumar gobara" a ma'ajiyar makamai sai dai ya yi kira ga mutane da su kwantar da hankulansu.
Wani babban jami'in soja, wanda ba ya so a ambaci sunansa, ya shaida wa AFP cewa "babbar ma'ajiyar makamai da ke N'Djamena ta kama da wuta".
Makamai daban-daban sun kama da wuta
Ma'ajiyar makaman tana maƙwabtaka da gidaje da dama na jama'a, kuma tana tsakanin filin jirgin saman ƙasa da ƙasa da wani sansanin sojojin Faransa.
Gobararar ta sa "dukka na'ukan makaman da ke ma'ajiyar sun kama da wuta", a cewar wani jami'i sojojin Faransa a hira da AFP ko da yake ba ya so a ambaci sunansa.
Wani mazaunin yankin ya ce ya ga mutum uku da suka jikkata a kan titi, kuma an garzaya da biyu daga cikinsu asibiti a kan babura.
Kafafen watsa labarai sun wallafa hotunan ƙwanson makamai da suka faɗa gidajen jama'a. Wani mao shago da ke gudanar da sana'arsa a yankin ya mutu bayan wani makami ya doke shi.
"Wata babbar ƙara ta abubuwan fashewa ta tashe mu daga barci," a cewar wani mazaunin yankin mai suna Moustapha Adoum Mahamat a hira da kamfanin labarai na Reuters ta wayar tarho.
"Gidanmu ya riƙa girgiza kamar wani yana harbinsa. Daga nan muka ga wata mummunar gobara ta tashi a sansanin sojoji sannan hayaƙi ya turniƙe sararin samaniya," in ji shi. "Mun riƙa ganin manyan makamai suna tashi sama."
Wani ganau ya shaida wa Reuters cewa ya ga curin hayaƙi yana tashi sama sannan ya ji ƙarar fashewar abubuwa ta kusan awa ɗaya kana hayaƙin ya watsu zuwa wasu sassan birnin.