'Yan ta'addar al-Shabab sun sha kai wa Mogadishu hari. Hoto: Wasu  

Adadin mutanen da suka mutu sakamakon tashin bam a wani gidan cin abinci da ke Mogadishu babban birnin ƙasar Somaliya ya haura zuwa mutum tara, kamar yadda majiyoyin tsaro suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP a ranar Litinin.

Lamarin ya faru ne bayan da wata mota maƙare da bam ta tarwatse a gidan abincin inda masoya ƙwallon ƙafa da suka je kallon wasan ƙarshe na gasar cin kofin nahiyar Turai ta Euro 2024.

''Fararen-hula 9 ne suka mutu, yayin da mutum 20 kuma suka jikkata sakamakon tashin bam ɗin,'' a cewar wani jami'in hukumar tsaron ƙasar Mohamed Yusuf, adadin da ya ƙaru daga mutum biyar da hukumomi suka sanar ranar Lahadi da daddare.

"Akwai mutane da dama a wurin cin abincin, yawancinsu matasa ne da ke kallon wasan ƙwallon kafa. Muna godiya ga Allah kan cewa mafi yawansu sun samu hanyar fita da ransu cikin lafiya bayan da suka yi amfani da tsani wajen haurawa ta bayan katangar ginin wurin," in ji shi.

Ƙarƙashin ɓaraguzan ginin

Hotunan da aka wallafa a shafukan intanet sun nuna yadda wuta da hayaƙi suka turnuke sama bayan da bam ɗin ya tashi a cikin shahararren wurin cin abinci da ke tsakiyar birnin.

Wani ɗan sanda Mohamed Salad da ya gane wa idonsa lamarin da ya faru 'yan mintoci kaɗan bayan tashin bam ɗin ya shaida wa kamfanin dillacin labaran AFP cewa an gano gawawwaki da dama a ƙarƙashin ɓaraguzan ginin.

''Mutane biyar ne suka mutu a wajen ginin da kuma kan babban titi ciki har da direbobin motocin da ke wucewa ta hanyar wurin da lamarin ya auku,'' in ji shi.

Munanan ayyukan ta'addanci

"Mutane huɗu ne suka mutu a cikin gidan abincin, an ciro wasu daga cikin ɓaraguzan gini," in ji jami'in.

Kawo yanzu dai babu wata ƙungiya da ta dauki alhakin kai harin, amma kamfanin dillancin labarai na ƙasar Somaliya ya ce mayaƙan ƙungiyar ta'addanci ta Al-Shabaab ne suka kai harin.

Ƙungiyar Al-shabaab dai ta shafe fiye da shekaru 17 tana kai hare-haren ta'addanci kan gwamnatin Somaliya a Mogadishi da wasu sassan ƙasar.

AFP