Fadan da aka gwabza a ranar Lahadi ya yi sanadin rufe wata babbar hanyar gabar ruwa da ta hada Zawiya da wasu biranen yammacin kasar Libya. / Hoto: Reuters

An yi arangama a ranar Lahadi tsakanin wasu kungiyoyi masu dauke da makamai a wani birni da ke yammacin kasar Libya, lamarin da ya yi sanadiyar hana mutane fita daga gidajensu tare da haddasa gobara a matatar mai ta biyu mafi girma a kasar, in ji jami'ai.

Fadan da aka gwabza a birnin Zawiya da ke gabar teku, mai tazarar kilomita 47 (kimanin mil 30) yamma da Tripoli babban birnin kasar, ya faru ne tsakanin 'yan bindiga masu biyayya ga kabilar Shurafaa da Mohamed Kushlaf, kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka bayyana.

Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya sanya wa Kushalf takunkumi a shekarar 2018 bisa zarginsa da hannu a safarar bil’adama.

Ba a dai san ko me ya janyo fadan ba amma ba sabon abu ba ne a yammacin Libya, wanda ke karkashin ikon mayakan sa-kai da kungiyoyi masu dauke da makamai da ke kawance da gwamnatin Firaminista Abdul Hamid Dbeibah.

Harin bindiga 'ta ko ina'

Kasar Libya mai arzikin man fetur dai ta shafe shekaru tana fama da rikici tsakanin gwamnatocin gabashi da yamma. Ta fada cikin rudani bayan boren 2011 da ya rikide zuwa yakin basasa, wanda ya kifar da gwamnatin Moammar Gadhafi da kuma kashe shi daga bisani.

A daidai lokacin da ake wannan rikicin, mayakan sun samu ƙarin dukiya da kuma iko, musamman a Tripoli da yammacin kasar.

Fadan da aka gwabza a ranar Lahadi ya yi sanadin rufe wata babbar hanyar gabar ruwa da ta hada Zawiya da wasu biranen yammacin kasar Libya.

“Iyalai da yawa sun makale a gidajensu. Ana harba harsasai ta ko ina, suna kai wa gidaje da gine-gine hari,” in ji Ahmed Abu Hussein mazaunin yankin na wata tattaunawa da shi,

AP