Wata rundunar haɗin gwiwa ta sojoji da hukumar tsaro ta farin kaya, DSS a Nijeriya sun yi nasarar daƙile wani yunƙurin kai hari da masu tayar da ƙayar baya da ake zargin ƴan Boko Haram ne suka yi a Jihar Kano.
“A wani samame da aka kai maɓoyar ƴan ta’addar da safiyar Juma’a 3 ga watan Nuwamban 2023, dakarun rundunar sojin Nijeriya ta 3 Brigade tare da haɗin gwiwar DSS, sun kai wani shiryayyen samame a ƙaramar hukumar Gezawa da ke Jihar Kano,” a cewar sanarwar da Daraktan hulɗa da jama’a na rundunar sojin Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya fitar.
Sanarwar ta ce an kai samamen ne da nufin gano da kuma kama ƴan Boko Haram bayan yin amannar cewa suna shirya kai wani gagrumin hari a Jihar Kano.
“Ba tare da ɓata lokaci ba sai dakaru suka ɗauki mataki inda suka kama mutum biyu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne waɗanda a yanzyu ake tsare da su,” in ji sanarwar.
Wannan lamari na zuwa ne kwana huɗu bayan da ƙungiyar ta kai wani harin da ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 40 a Jihar Yobe, kamar yadda ƴan sanda suka sanar.
Harin na Jihar Yobe ya zama wani gagarumi irinsa na farko da aka kai jihar a cikin wata 18 da suka wauce, kamar yadda ƴan sanda suka bayyana a ranar Laraba.
Makaman da aka kama a samamen Kano
Rundunar sojin Nijeriyar ta ƙara da cewa rundunar haɗin gwiwar ta sojoji da DSS ta ƙwato bindiga AK 47 guda biyar da jigidar harasan AK 47 din biyar da na’urar harba rokoki da gurneti da kakin soji da bama-bamai da sauran munanan makamai.
“Hadin gwiwar rundunar sojin da ta sauran hukumomin tsaro babban misali ne na gudanar da aiki bisa tsari, da kuma nuna ƙarfin ƙoƙarinmu don magance ta’addanci da sauran matsalolin tsaro.”
Nasarar da aka yi a samamen ta jaddada ƙoƙarin rundunar sojin na kare rayuka da dukiyoyin ƴan ƙasa.
“Rundunar sojin Nijeriya za ta ci gaba da ƙoƙarin yaƙi da kuma durƙusar da ta’addanci da sauran matsalolin tsaro a faɗin ƙasar.
A ƙarshe rundunar sojin ta yi kira ga jama’a da su dinga taka tsantsan tare da haɗa kai da rundunar da sauran hukumomin tsaro don samar da ingantattun bayanan da za su taimaka a ayyukan magance matsalar tsaro da ake yi.
“Rundunar sojin Nijeriya tana jadadda sadaukarwarta don kare ƙasarmu da kuma neman goyon bayan mutanenta.”
Boko Haram
Ƙungiyar Boko Haram ta sha kashe mutane da sace su a Jihar Borno, inda a can suka fi aiwatar da ayyukansu tsawon shekara 14.
Kungiyar ta fara ayyukanta ne a shekarar 2009, inda ta kashe dubban mutane tare da raba dubbai da muhallansu, lamarin da ya sa aka shiga cikin mummunan yanayin jinƙai musamman a jihohin Borno da Yobe.
Bayan mutuwar shugabanta na biyu Abubakar Shekau a watan Mayun 2021, sai ƙungiyar ta shiga ruɗanin shugabanci, inda aka samu rarrabuwar kai a cikinta.
Hakan ya yi tasiri sosai wajen rage ƙarfinta, sannan kuma ƙoƙarin gwamnatin Nijeriya da daƙile ayyukanta ma ya sake rage mata ƙarfi.