Ana yi wa wani mutum allurar riga-kafin cutar Mpox, a babban asibitin da ke Goma, Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo ranar 5 ga Oktoban 2024. / Hoto: AP Archive

Cutar Farankamar Biri wato Mpox har yanzu babbar matsalar kiwon lafiyar jama'a ce a Afirka, in ji shugaban Cibiyar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa ta Afirka (Africa CDC) a ranar Alhamis, yayin da ake samun sabbin masu kamuwa da cutar.

Jean Kaseya ya fada a wani taron manema labarai cewa an samu sabbin mutane 3,186 da suka kamu da cutar a cikin makon da ya gabata, inda aka tabbatar da 489 sun kamu, sannan 53 suka mutu.

"Ba mu ga raguwar mace-mace ba, amma muna ganin ƙaruwa idan muka kwatanta da makonnin da suka gabata," in ji shi, ya ƙara da cewa akwai bukatar hanzarta daukar matakai da dama, ciki har da allurar rigakafi, don dakatar da yaduwar.

A cikin 2024, sama da mutum 38,300 ne alkaluma suka nuna sun kamu a cikin ƙasashe 16 na nahiyar, inda mutum 979 kums suka mutu, bisa ga sabbin bayanai daga Afirka CDC.

Ghana da Zambia su ne kasashe na baya-bayan nan da suka bayar da rahoton bullar cutar mpox a nahiyar.

Gaggawar lafiyar jama'a ta duniya

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ayyana Mpox a matsayin gaggawar lafiyar jama'a a cikin watan Agusta a karo na biyu cikin shekaru biyu, biyo bayan yaduwar wani sabon nau'in cutar daga Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo zuwa kasashe makwabta.

Kaseya ya ce, shirin riga-kafin da aka ƙaddamar a karshen makon da ya gabata a DRC, kasar da ta fi fama da cutar a yankin yana kan hanya, inda aka yi wa mutane sama da 1,600 allurar riga-kafin, musamman a gabashin kasar.

Nijeriya, wacce ta samu kason allurai 10,000 na alluran riga-kafi daga Amurka, za ta fara allurar a cikin kwanaki masu zuwa, a cewar cibiyar kula da lafiya ta Africa CDC.

Afirka na fatan samun allurai miliyan 10 daga abokan hulda.

Cutar Mpox na nuna alamun mura da raunuka masu cike da kumburi.

AA