Attajirin Kongo, Moïse Katumbi, wanda ya dade yana adawa, zai yi takarar shugaban kasar a karon farko, shekara biyar bayan gwamnati mai ci ta hana shi takara.
A zaben na shugaban kasa 'yan takara 22 ne za su fafata bayan da yunkurin hada kan Katumbi da sauran 'yan adawa domin tunkarar Shugaba Felix Tshisekedi ya ci tura.
A yakin neman zaben, Katumbi ya yi alkawarin 'yanta kasar bayan zabe idan an zabe shi.
Amma masu suka sun nuna shakka kan dacewarsa da shugabancin kasar, suna masu ikirarin cewa babansa ba dan asalin Kongo ba ne.
Babansa, Nissim Soriano, dan asalin kasar Girka ne. Ya koma Congo ne a lokacin yakin duniya na biyu bayan tserewa daga Rhodes kuma ya nemi mafaka a yankin Kashobwe, kusa da Zambia, inda ya fara kasuwancinsa na kifi.
A nan aka haifi Katumbi a ranar 28 ga watan Disamba a shekarar 1964. Mahaifiyarsa, Virginie Mwende, 'yar asalin kasar Kongo ce.
"Suna karya," kamar yadda yake fada da yakini a lokacin yakin neman zabesa, "Ni dan Kongo ne, kuma wannan kasar ƙasata ce."
Tarihin kasuwancinsa
Katumbi wanda ya taba kasancewa tsohon gwamna a wani lardin kudancin kasar, ya fara kasuwanci ne a lokacin da yake makarantar sakandare yayin da ya fara shiga harkar kifin babansa, kafin ya shiga harkar noma da sufuri da kuma harkar haƙar ma'adinai.
"Na yi aiki tukuru a rayuwata. Da na so in yi karatu a jami'a, amma na fi sha'awar kasuwanci a rayuwata," in ji shi.
Kawo yanzu dai ba a san nawa yake da shi ba, amma a shekarar 2007, kafin ya zama gwamnan lardin, Katanga ya ce kamfaninsa na da jarin dala miliyan 400.
Masu sharhi kan lammuran siyasa a Kongo, sun ce arzikinsa mai dimbin yawa zai iya kasancewa muhimmin abin da zai ciyar da takararsa gaba.
"Yana yakin neman zabe kamar yadda yake kasuwancinsa, ba tare da kau da kai kan komai ba. Ya samu lokacin shiryawa da kuma kafa shirye-shiryen kamfe dinsa," a cewar Yves Kasongo daga garin kudanci na Lubumbashi.
An tuhumi Katumbi da laifin ƙwace fili da kuma daukar mayakan haya. Ya tsere daga kasar zuwa Afirka ta Kudu.
An hana shi takarar shugaban kasa a shekarar 2018 kuma ya koma Kongo ne a shekarar 2019 bayan jam'iyyarsa ta hade da gamayyar jam'iyyun Tshisekedi masu mulki.
Mai sha'awar kwallon kafa
Tun shekarar 1997, Katumbi yana daya daga cikin kungiyoyin kwallon kafar da suka fi karfi a kasar - Tout Puissant Mazembe, wadda aka fi sani da TP Mazembe.
Kungiyar ta lashe kofin Afirka guda biyar, ciki har da kofin zakarun Afirka uku (a shekarar 2009 da shekarar 2010 da kuma shekarar 2015) karkashin jagorancin Katumbi.
Nasarorin da ya samu a kasuwanci sun sa ana sukarsa cewa "ya fi bai wa cin riba muhimmanci bisa komai".
Amma Katumbi ya bayyana nasarorinsa na gwamnan lardi a matsayin hujjar iya mulkinsa ciki har da nasarorin gina hanyoyi, kafa makaranti da kuma habaka harkar noma.
Yana kamfe kan yin garambawul wa hukumomi da habaka tattalin arziki ta hanyar samar wa Kongo hukumomi masu karfi tare da yaki da cin hanci da rasahawa.
Ya sha alwashin samar da ayyukan yi sama da miliyan uku da gina ajujuwa 50,000 tare da daukar malamai 15,000 aiki a fadin kasar idan aka zabe shi.
Ya kuma yi alkawarin gina hanyoyi na tsawon kilomita 28,000 tare da samar da ruwan sha mai tsafta ga dukkan 'yan kasar.