Sojojin Nijar na tsare da Mohamed Bazoum tun bayan da suka hambarar da gwamnatinsa a watan Yuli,/Hoto: Reuters

Sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar sun ce sun dakile wani yunkuri da hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum ya yi na tserewa daga kasar.

Sun bayyana haka ne a wata sanarwa da suka karanta a gidan talbijin na kasar ranar Alhamis da maraice.

Bazoum yana tsare a hannun sojin da suka kifar da gwamnatinsa ranar 26 ga watan Yuli duk da cewa kasashen duniya sun yi ta kiraye-kirayen sakinsa.

Mai magana da yawun gwamnatin sojin Kanar-Manjo Amadou Abdramane, wanda ya bayyana hakan jawabin da ya yi wa 'yan kasar, ya ce Bazoum da iyalansa da taimakon wasu jami’an tsaro, sun kitsa tserewa ta hanyar tuka shi zuwa wajen birnin Yamai babban birnin kasar, inda daga nan zai shiga jirgi mai saukar ungulu zuwa Nijeriya mai makwabtaka.

Ya kara da cewa Bazoum ya yi kokarin tserewa da karfe uku na safiyar ranar Alhamis tare da iyalansa da masu dafa masu abinci biyu da kuma jami’an tsaro guda biyu.

Labari mai alaka: Sojojin Nijar sun kama manyan jami'an gwamnatin Bazoum

"Matakin gaggawa da jami’an tsaro suka dauka ya sa sun iya dakile yunkurin wanda aka shirya shi don kawo rudani a kasarmu," in ji Kanar-Manjo Abdramane.

Sai dai ba a ji martani daga bangaren hambarar Shugaba Bazoum ba, wanda har yanzu ba a san inda yake ba.

Juyin mulkin da aka yi a Nijar shi ne na biyar a yankin Yammacin Afirka a cikin shekara uku.

Kamar yadda aka hambarar da zababbun shugabanni a Mali da Burkina Faso, sojoji sun ce sun hambarar da Bazoum ne saboda ci gaba da karuwar rashin tsaro da ya yi sanadin mutuwar dubban mutane a yankin, wanda sojojin suka ce za su iya magancewa fiye da gwamnatin farar hula.

’Yan jam’iyyar Bazoum da iyalansa sun ce an yanke masa ruwa da wutar lantarki, abin da ya jawo Allah-wadai daga kasashen yammacin duniya, tsofaffin kawayen Nijar.

TRT Afrika