Daga Abdulwasiu Hassan
Gwamnatin Jihar Legas a Nijeriya, yanki mai dimbin jama'a, na fama da datti da bola da ke addabar mazaunan jihar tare da gurbata muhalli. Babbar sharar da ta fi damun jihar ita ce kwalaben roba da ake zubarw aa kan tituna da cikin teku.
A baya-bayan nan gwamnatin ta sanar da haramta amfani da kwalaben roba da kwanon soyoyo na zuba abinci, a matsayin wani bangare na matakan magance matsalar da ta munana tsawon shekaru.
Wasu na bayyana cewa wannan mataki bai zo rana guda ba. Wasu kuma na kira da a samar da mafita kafin aiwatar da wannan haramci.
A matsayin ta na jiha mafi cunkoson jama'a a Nijeriya, Legas ta shirya rayuwa ba tare da kwalaben roba da mazubin abincin soyoyo ba, an samu rarrabuwar ra'ayin jama'a kan haramta samarwa da sayar da wadannan abubuwa biyu.
Ga jihar da samun tarin sharar kwalaben roba har tan 870,000 a shekara, watakila matakin farko na haramci, saboda yadda yawaitar jama'a kan iya sanya abubuwa su fi karfin yadda za a magance su.
Da yake sanar da haramcin ta shafinsa na X, kwamishinan muhalli da albarkatun ruwa na Jihar Legas, Tokumbo Wahab ya shaida cewa an dauki matakin ne saboda matsalar gurbata muhalli da robobi ke yi.
Wannan mataki na haramci na farko a Nijeriya ya janyo mayar da martani daban-daban.
"Haramcin kwalaben roba da mazubin abinci na soyoyo ya yi daidai da kokarin da duniya ke yi na yaki da gurbata muhalli da roba ke yi, da kuma tabbatar da kyakkaywan muhalli mai dore wa," in ji Alex Akhibe, wand aya samar da wata kungiya ta kare muhalli mai sunan, African Cleanup Initiative yayin da yake tataunawa da TRT Afirka.
Ya ce "Hakan na nuni da kokarin magance matsalolin muhalli da kuma karfafa gwiwar amfani da wasu abubuwan da suka fi alfanu ga muhalli. Wannan cigaba ne mai kyau da z aa amince da shi."
Amma ba kowa ne ya amince da Alex ba game da wannan haramci. A yayin da wasu ke ganin tuntuni ya kamata a ce an aiwatar da hakan, wasu kuma ba su da tabbacin ko mahukunta sun yi daidai wajen saka haramcin, kafin a ce an samar da wasu kayan da za su maye gurbin robobin.
Tsaunin shara
Abun da babu mai gardama a kai shi ne hada-hada da ake samu a garin na gabar teku da ya zama babban birnin kasuwancin kasa mafi karfin tattalin arziki a Afirka. Jihar Legas na da fadin kasa mai girman sukwayamita 3,577, ind atake dauke da kusan mutane miliyan 21.
Yawan jama'a na ci gaba da daduwa, a yayin da kowa ke kokarin amfana da hada-hadar da ake yi a garin.
Duk da cewa Legas na da wajen ajje shara kamar su Olusosun da Epe, wannan bai wadatar ba.
Tare da yawiatar jama'a, jihar na bukatar karin sarari don samar da gidaje, wanda wannan ma wani kalubale ne na samar da karin wuraren tara shara musamman kwalaben roba da mazubin abinci na soyoyo.
Legas ba ta da tsarin sabunta irin wadannan bolar ta robobi, amma babban ɓangaren sharar ya ragu a wuraren da ake zubarwa. Sannan ba a sabunta robobi da ledoji da ake zuba abinci a cikinsu.
Kalubalen dabbakawa
Hukumar Kula da Sharar ta Legas (LAWMA) ta bukaci mazauna yankin da su yi amfani da wasu hanyoyin da za a sake amfani da bolar maimakon robobi da aka hana amfani da su don yaki da sauyin yanayi da ambaliyar ruwa da cututtukan da ke da alaka da sharar robobi.
LAWMA ta ce sashen tabbatar da kare muhalli mai suna KAI zai taimaka wajen aiwatar da dokar. Wasu gidajen abinci a jihar sun fara bin sabbin dokokin.
Kantin sayar da abinci na Chicken Republic a Legas, ya sanar da cewa shagunansa da ke birnin za su fara sauya sheƙa daga amfani da robobi don zuba abincin masu saya su tafi da shi. “Muna karfafa gwiwar ‘yan kasarmu a fadin jihar nan da su kawo robobin abinci da za a iya sake amfani da su,” in ji kamfanin.
Masu ruwa da tsaki na ganin akwai bukatar wayar da kan jama'a sosai game da mummunan tasirin da robobi ke yi a kan muhalli, tare da jaddada fa'idar bin dokar.
Alex ya ba da shawarar cewa ya kamata hukumomi su "inganta da tallafawa da haɓakawa da kuma amfani da hanyoyin da za su dace da muhalli maimakon robobi, wanda zai sa su kasance masu sauƙi kuma masu araha ga 'yan kasuwa da masu siye".
Gwaji
Duk da kyakkyawan fata game da haramcin, masana na ganin akwai wata hanya da gwamnatin jihar za ta bi wajen aiwatar da shi tare da karfafa shirin sake amfani da su.
"Tasirin aiwatar da dokar ya dogara ne da abubuwa daban-daban, kamar matakin wayar da kan jama'a da yawan kokarin da za a yi a aiwatar da shi, da kuma samar da wasu kayayyaki," Alex ya shaida wa TRT Afrika.
Ya kara da cewa, “Ya kamata gwamnati ta yi ta wayar da kan jama’a domin jama’a da dama su san dokar da kuma yin aikinsu.
Wani abin kuma si ne ukumomi na bukatar mayar da ankali wajen karfafa gwiwar ba da tukwuci ga masu bin tsarin sabunta shara. Wani ƙalubalen kuma shi ne kwashe bola daga magudanan ruwa da hanyoyin ruwa a Legas.
"Duk magudanan ruwa da muka tsaftace a lokacin wani aikin tsaftacewa na baya-bayan nan an cika su da robobi da ledoji. Don haka, tilasta dokar hana amfani da robobi da ledoji dole ne ya zama sai an saka ƙwanji sosai," in ji Alex.