Tallafin abinci na ‘yan gudun hijirar Sudan sama da rabin miliyan a Chadi zai kare a watan gobe ba tare da samun wasu tallafin kudade ba, a cewar jami’in Hukumar Abinci ta Duniya WFP a ranar Laraba.
"Ya zuwa watan Disamba, babu wani taimako da ake sa ran samu," in ji Pierre Honnorat, daraktan Hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya MDD a kasar Chadi, a yayin hirarsa da kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Ya kara da cewa "Muna kira da a gaggauta kawo agaji tun daga yanzu."
'Yan gudun hijirar Sudan sama da 540,000 ne suka tsallaka zuwa Chadi tun bayan yakin da ya barke watanni 7 da suka gabata tsakanin sojojin kasar da dakarun RSF, a cewar Hukumar Kaura ta Duniya (IOM).
Da dama da cikinsu sun tsere ne daga Yammacin Darfur, inda rikicin kabilanci da kuma kashe-kashen jama'a suka sake barkewa a watan nan a El Geneina babban birnin jihar, lamarin da ya tilasta wa dubban mutane tserewa.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya fitar da wani rahoto da ke cewa tsakanin watan Afrilu zuwa Yunin shekarar nan dakarun RSF da mayakan sa-kai na kawancen Larabawa sun kwashe makonni suka kai hare-hare kan Masalit, kabila mafi rinjaye a El Geneina.
Karanta labari mai alaka: Harkokin ‘yan gudun hijira a Chadi 'za su lashe $140m a wata shida'
Wadanda suka isa a wannan shekarar sun hadu da sauran 'yan gudun hijirar da kuma mutanen da suka rasa matsugunansu da tuni suke tsugune a sansanonin Chadi, a cikin yanayin da Honnorat ya bayyana na ''tsananin matsi''.
"Yanzu lokacin sanyi ne, amma duk da haka yanayin da matukar zafi," in ji shi. "Ga kuma matsalar abinci mai gina jiki da ke zama tashin hankali."
"Muna bukatar akalla dala miliyan 25 a kowane wata don taimakawa wajen samar da abinci a kullum ga kusan mutum 800,000 da muke kokarin yi musu hidima," a cewar Honnorat.
Rikicin Sudan ya ta'azzara matsalar yunwa a fadin kasar.
A ranar Laraba Hukumar Abinci da Aikin Noma ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta raba iri na hatsi da zai iya ciyar da mutum miliyan 13 zuwa miliyan 19, sakamakon irin barnar da yakin ya yi a ayyukan noma na kasar.
Fiye da mutane miliyan 20 daga cikin al'ummar Sudan mutum miliyan 49 ne suke fuskantar matsalar karancin man fetur bisa ga binciken Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyi masu zaman kansu da sauran hukumomi suka yi.