Mayaƙan rundunar kai ɗaukin gaggawa ta RSF a Sudan sun kashe mutane fiye da 200 ciki har da mata da ƙananan yara a farmakin da suka kwashe kwanaki uku suna kai wa wasu ƙauyuka a kudancin ƙasar, a cewar wata ƙungiyar lauyoyi da ke sanya ido kan yaƙin da ke faruwa a ƙasar.
Rundunar Rapid Support Forces (RSF), wadda ta kwashe shekara biyu tana gwabza yaƙi da dakarun Rundunar Sojin Sudan (SAF), sun "kai hari kan fararen-hula da ba sa ɗauke a yankunan da babu sojoji" a ƙauyukan Al-Kadaris da Al-Khelwat da ke jihar White Nile, a cewar ƙungiyar Emergency Lawyers, wadda ke tattara bayanai game da take hakkokin bil'adama da ake yi a Sudan.
Ta ƙara da cewa mayaƙan RSF sun "kashe tare da sace da kuma ɓatar da mutane sannan sun sace kayansu" lokacin harin da suka ƙaddamar tun daga ranar Asabar, kana sun jikkata ɗaruruwan mutane.
Sudan ta faɗa cikin rikici tun watan Afrilun 2023, bayan saɓanin da aka samu tsakanin shugaban mulkin sojin ƙasar Abdel Fattah al-Burhan da tsohon mataimakinsa kuma shugaban rundunar RSF Mohamed Hamdan Daglo.
Yaƙin ya yi sanadin mutuwar dubban mutane, tare da raba mutum fiye da miliyan 12 da muhallansu.