Jihar Borno na daga cikin jihohin Nijeriya da ke fama da matsalar rashin tsaro. / Hoto: Reuters

Wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun kai hari ofishin ‘yan sanda na Jakana da ke Ƙaramar Hukumar Konduga ta Jihar Borno inda suka kashe ɗan sanda ɗaya da wata mace.

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa maharan sun gudu da makaman ‘yan sandan sannan kuma ƙona motocin sinitiri biyu na ‘yan sandan da babur ɗaya.

Jaridar Daily Trust a Nijeriya ta ruwaito cewa maharan sun kai harin ba-zata inda suka isa ofishin ‘yan sandan da misalin ƙarfe ɗaya na dare sannan suka yi ta musayar wuta da ‘yan sandan har zuwa uku na dare.

Majiyar ta bayyana cewa maharan sun sha ƙarfin ‘yan sandan inda suka afka cikin ofishin nasu suka ƙona motocin sinitiri biyu wadda ɗaya ta ‘yan sanda ce ɗaya kuma ta ‘yan banga.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Konduga, Honarabul Abbas Ali Abari ya tabbatar wa ‘yan jarida kai wannan harin sai dai bai yi ƙarin bayani ba.

TRT Afrika ta yi ƙoƙarin samun ƙarin bayani daga mai magana da yawun ‘yan sandan Borno Nahun Keneth sai dai wayarsa a kashe.

Jihar Borno ta kwashe shekaru da dama tana fama da hare-haren 'yan Boko Haram waɗanda suka yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba miliyoyi da muhallansu.

Ko a watan da ya gabata sai da aƙalla mutum 32 suka rasu bayan wata 'yar ƙunar-baƙin-wake ta tashi bam ɗin da ke jikinta a Ƙaramar Hukumar Gwoza ta Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya.

TRT Afrika da abokan hulda