Matatar fetur ta Dangote ta fara samar da dizel da man jirgin sama

Matatar fetur ta Dangote ta fara samar da dizel da man jirgin sama

Rukunin Kamfanonin Dangote ya ce matatar man tana iya fitar da tankokin mai 2,900 a kowace rana.
Alhaji Aliko Dangote ya ce matatar man fetur din za ta samar da "dubban" ayyukan yi ga matasan kasar. /Hoto: Reuters

Matatar fetur ta hamshakin dan kasuwar nan na Nijeriya Alhaji Aliko Dangote ta soma samar da dizel da man jiragen sama.

Wata sanarwa da Rukunin Kamfanonin Dangote ya fitar ranar Juma'a ta ce matatar ta bayyana "matukar farin ciki" na fara gudanar da wannan aiki da zai bunkasa tattalin arzikin Nijeriya da ma sauran kasashen Afirka.

"Matatar man tana iya yin lodin tankokin mai 2,900 a kowace rana. Man da matatar za ta samar zai dace da dokokin kare muhalli. An gina mamatar ne bisa dokokin Bankin Duniya da Hukumar Kare Muhalli ta Amurka da ta Turai" na rage gurbata muhalli.

Dangote ya gode wa shugaban Nijeriya Bola Tinubu da gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu da sauran masu ruwa da tsaki bisa hadin kan da ya samu wajen aiwatar da wannan gagarumin aiki.

“Wannan babbar rana ce ga Nijeriya. Muna matukar farin cikin kai wa wannan babban matsayi. Wannan babbar nasara ce ga kasarmu domin kuwa ta nuna azamarmu wajen aiwatar da manyan ayyuka. Wannan zai kawo gagarumin sauyi a kasarmu," in ji sanarwar.

Bayanan da kamfanin Dangote ya fitar sun nuna cewa matatar ita ce daya tilo da ke da rariya mafi girma a duniya da za ta iya tace gangar mai 650, 000 a kullum./Hoto: Rukunin Kamfanonin Dangote/X

A watan Mayun 2023 aka kaddamar da matatar man ta Dangote a wani gagarumin biki da ya samu halartar shugabannin kasashen Afirka da dama.

Alhaji Aliko Dangote ya ce matatar man fetur din za ta samar da "dubban" ayyukan yi ga matasan kasar.

Bayanan da kamfanin Dangote ya fitar sun nuna cewa matatar ita ce daya tilo da ke da rariya mafi girma a duniya da za ta iya tace gangar mai 650, 000 a kullum.

TRT Afrika