Sherry Davis ta je gidajen tarihi da dama domin gudanar da bincike. Hoto/Sherry Davies

Karisa Ndurya ya shafe akasarin rayuwarsa yana tona kayayyakin tarihi na Afirka. Ya shafe sa’o’i da kwanaki da watanni a karkashin rana yana tono a Kenya, ba tare da cewa tarihi ba zai masa adalci ba.

Sama da shekara talatin bayan mutuwar mai tonon kayan, duniya ba ta taba tunawa da shi ba, kamar yadda jikarsa ta bayyana a kokarinta na sauya wannan lamarin.

A shekarun 1940, Karisa na daga cikin daya daga cikin rukunin wadanda suka yi aikin hakar kayan tarihi a Fort Jesus, wadda ganuwa ce magina ‘yan Afirka suka taimaka wa wadanda suka zo daga Portugal ginawa a tsibirin Mombasa na Kenya.

Aikin da ya yi a ganuwar da kuma sauran tone-tone a Kenya, ya dauki tsawon shekara 20, inda ya fito da bayanai kan tarihin Kenya, musamman ta hanyar tono kayayyaki daga wani wuri a Gedi.

Akasarin kayayyakin da aka tona daga cikin kasa a wurin da ya yi aiki na nan an ajiye su a gidajen tarihi a fadin duniya.

Amma a lokacin da Karisa ya rasu a 1988, ayyukansa da gudunmawar da ya bayar, da alama komai ya gushe.

Babu wani labari a game da shi ko kuma bayyana wani abu da ya yi a littattafan tarihi. Labarin Karisa ba kage bane.

Wannan ne abin da ya faru da daruruwan mutanen da aka bai wa kwangilar tone-tone a shekarun 1930 da 1940 da 1950.

Su suka yi duka wahalar amma ba su taba samun ladarta ba

Kamar Karisa Ndurya, Kamoya Kimeu da John Onyago ba a yaba musu kan aikin da suka yi ba. Hoto/Sherry Davies

Alkawarin jika

Sherry Davies, wadda mawakiya da marubuciya ce ta kasar Jamaica da Kenya, ta kudiri aniyar ganin Karisa ya samu yabo wanda ya dace.

“Na san cewa kakana ya yi aiki a wuraren hakar kayan tarihi a Kenya, sai dai ganin cewa ba a taba bayyana shi a matsayin wanda ya bayar da gudunmawa ba babu adalci. Lamari ne mai zafi,” kamar yadda Sherry ta shaida wa TRT Afrika.

A 2018, Sherry ta bar wakokin da take yi domin soma ayyukan farfado da sunan kakanta da sauran wasu masu ayyuka irin nasa na hakar kayan tarihi.

“A lokacin da na kai ziyara Fort Jesus da ke Mombasa, sai na lura an rubuta sunan mai gidan su kakana (James Kirkman) a bangon ganuwar baki daya, amma babu sunan ‘yan Afirka,” kamar yadda ta bayyana.

James Kirkman da Chimera Chizingo a Fort Jesus a shekarun 1950. Hoto/Sherry Davies

“Na je wurin ajiye littattafai na gidan tarihin inda na ga kundin tarihi inda na kalli irin hotunan da ke jikin jaridun lokacin na shekarar 1940 da 1950.

Dukansu sun mayar da hankali kan farar fata masu hakar ma’adinai, inda suke kallon aikin Turawa.

“Babu ‘yan Afirka a cikin labarin”. Sai Sherry ta fusata inda ta nemi ta samu karin bayani dangane da kakanta.

“Sai na shaida wa kaina, “Tabbas wannan bayanin na nan a waje. Dole wani yana da labarin kakana da sauran mutane ‘yan kasa wadanda suka bayar da gudunmawa matuka wurin hakar ma’adinai a Kenya”.

Sherry ta zagaya gidajen tarihin Kenya da wuraren da masu hakar kayan tarihi suka tono, inda ta tafi da mai daukar hoto domin ajiye su da yin wani dan kwarya-kwaryar fim domin wallafawa a kafafen sada zumunta.

“A gajeren bidiyon ne wanda na wallafa a Youtube na nemi taimako. A nan ne na yi tambaya kan idan da duk wani mai bayani ko amsa ko hanyar da za a samu wani bayani na ‘yan Kenya kamar kakana wadanda suka yi aiki a wuraren farko na hakar kayan tarihi,” kamar yadda ta tuna.

Karisa Ndurya da wasu a wuraren hakar kayan tarihi na Fort Jesus. Hoto/Sherry Davies

“Mutane sun rinka kira inda suke bayar da hotuna na ‘yan Afirka wadanda suka yi aikin hakar kayan tarihin inda aka gano su. Haka kuma wasu da suka ce iyayensu sun yi aiki a wuraren hakar kayan tarihin a Kenya sun neme mu,” in ji ta.

Hotuna na bayar da labari

Hotunan na daukar hankali kuma su ne hujjojin da suka rage ga ‘yan Afirka wadanda za su nuna cewa sun taka muhimmiyar rawa wurin hakar kayayyakin tarihi a Kenya. “Wadannan hotunan sun amsa tambayoyi da dama da na rike tsawon shekaru.

Koyon tarihina na Afirka, da kawar da kaina daga Tunanin Turai wanda na girma da shi, da kuma tafiya gano tarihin kakannina yana da kyau,” in ji Sherry.

A yanzu, da hadin gwiwar gidajen tarihin Mombasa da ke Landan, Sherry na ta bayyana wasu sunaye na wadanda suka yi ta aikin hakar kayayyakin tarihi wadanda ta gano a lokacin bincikenta.

Sherry ta bayyana wani bincike da ta yi mai taken ‘Ode to the Ancestors’, daga ciki har da hotunan da ba a saba gani ba wadanda aka saka a wuraren tarihi na Landan da Kenya a shekarun 2023.

Lokaci ne na jin dadi a gareta da abokan aikinta, wadanda suka yi aiki tukuru domin shawo kan kalubalen da ake fuskanta.

Sherry da iyalanta a Fort Jesus. Hoto/Sherry Davies

“Mun fuskanci kalubale daga kungiyoyin al’adu da wuraren karatu wadanda suka ki amincewa su ba mu damar duba rumbunsu.

Da dama sun ki amsa kiranmu. Mutanen da suke da bayanai masu kyau wadanda za su iya daukar mu shekaru muna bincike sun ki taimakonmu,” in ji ta.

“Wannan duk sakamakon farar fata ne da ke kula da wadannan kamfanonin, kuma suna tunanin muna sukar masu hakar kayan tarihi farar fata wadanda suka yi aiki da takwarorinsu bakar fata.”

Sherry ta dage kan cewa ba wannan ce manufarta ba.

“Ina so ne kawai na san dalilin da ya sa masu hakar kayan tarihi farar fata suka samu yabo, sai kuma bakar fata wadanda suka yi aiki da su ba a ko bayyana sunayensu a kundin tarihi ba,” kamar yadda ta bayyana.

Hoton Karisa Ndurya wanda shi ne kakan Sherry. Hoto/Sherry Davies

Wannan amsa ce wadda Sherry ba ta taba samu ba. Akwai kuma bukatar ta nemi taimako kafin sanin duka hotunan da ta samo.

“Abin takaici, akwai wasu hotunan bakaken fata da ba za mu taba iya gano su ba. Akwai wani muhimmi wanda aka dauki hotonsa daga baya tun daga can nesa,” in ji shi.

“Mun shirya ƙirƙirar bayanan wasu daga cikin waɗannan ƙwararru waɗanda muka gano don tabbatar da cewa har abada suna nan a Wikipedia da intanet da ƙungiyoyin tarihi waɗanda muke aiki da su," in ji ta.

A yanzu da lamarin yake samun ci gaba, Sherry na son komawa kan abin da take so.

Sherry Davis da Mohammed Lugogo a wani gidan tarihi. Hoto/Sherry Davies

Sai dai a yadda take a matsayin jikar Karisa, za ta ci gaba da neman sunayen da aka danne game da masu hakar ma’adinai na wakoki.

TRT Afrika