Ga mai fentin dan Gabon Regis, fenti kan titi yana daga cikin siyasa. Hoto/ Régis Divassa 

Bangon da ke birnin ne wurin gudanar da fentinsa. Yana dauke da gwangwanayen gudanar da feshi, Regis Divassa na gararamba kan titunan Libreville babban birnin Gabon inda yake feshi da fentinsa.

Ya koya wa kansa aikin, kuma ya yarda da cewa karfin kimiyyarsa na tattare da gaskiyar cewa kowa yana da damar amfana, ba wai sai ‘yan boko ba.

“Ba kowa bane zai iya rubuta abin da muke rubutawa saboda ya danganta da irin yadda muka yi rubutun. Rubutun da ake yi da fenti ana yinsa ne ta yadda kowa zai iya karantawa a cikin sauki. Kamar yaro ne mai zuwa makaranta inda yake soma rubuta wani abu: a wani lokaci, ana iya gani, wani lokacin kuma ba a iya gani, kamar rubutun likitoci ne. Akwai masu rubutu da fenti da suke yi mai wahalar fahimta amma kuma akwai wadanda suke yin sa ba tare da wahala ba,” in ji Regis Divassa a tattaunawarsa da TRT Afrika.

Mai zanen yana amfani da zaben kan titi domin wayar da kan jama'a. Hoto/Régis Divassa 

A unguwar Akebe, sama da mutum daya cikin hudu da ke zaune a unguwar ba su da aikin yi.

Talauci da rikici na daga cikin rayuwar yau da kullum, sai dai ga masu rubutu da fenti kamar irin su Divassa, abin da ke gabansa shi ne amfani da launuka kullum a rayuwarsa.

“Zane da fenti da muke yi a yau dorawa ne kan wadanda suka gabace mu, shi yasa muke yi a bango sakamakon ya fi tasiri. Ba za ka iya daukar bango ka yi tafiya da shi ba, son kai ne boye fasaha. Ana so a rinka bayyana fasaha. A kan tituna, hanyar da za a iya bayyanata ita ce a bango kadai,” in ji shi.

Idan bai fita waje yana yin fenti kan tituna ba, Divassa yana yawan tunanin fenti daga dakinsa. Sakon da yake so ya isar a ranar shi ne: mata.

“Dole ne a ce mata su ne ginshiki, su ne ainahin fasaha, cikakkiyar siffar da Allah ya ba mutum. Don kada na zauna ni kadai, dole ne na yi fentin mata, alamun haihuwa. A gare ni, mata su ne misali mafi kyau, na fasaha,” in ji mai fentin.

Ayyukan Divassa sun jan hankali a babban birnin na Gabon. Hoto/Regis Divassa

Domin samun biyan bukata, yana amfani da wannan sana’ar domin yin aiki ga masu shaguna don shagunan su zama suna da jan hankali, sai dai bai shirya soma zane da fenti gadan-gadan ba, inda ya fi so ya tsaya kan wanda yake yi a bango.

“Rubutu da fenti shi ne makami mafi kyau, ya fi tasiri fiye da komai. Mai rubutu da fenti mutum ne wanda ya himmatu sosai: ta bangaren siyasa ko zamantakewa, mutum ne da yake bayarwa ko da ba ya so ya bayar, tamkar mutum ne ya yi wa kansa tawaye,” in ji Divassa.

A yau, sunansa ya zarce iyakar Gabon. A yayin da yake dauke da gwangwanayen fentinsa, ya fita domin mamaye sabbin bangwaye domin yi musu fenti.

TRT Afrika