Wasu da ake zargin 'yan tada kayar baya ne a tsakiyar kasar Mali na rike da fararen hula fiye da 110 da suka yi garkuwa da su kwanaki shida da suka gabata, kamar yadda wasu majiyoyin kasar suka shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa a ranar Litinin.
Wasu mahara sun tare motocin bas guda uku dauke da fararen hula a ranar 16 ga watan Afrilu, inda suka tilasta wa motocin da fasinjojin zuwa wani dajin da ke tsakanin Bandiagara da Bankass, kamar yadda wata kungiyar kungiyoyin yankin da wani zababben jami'in suka ce.
Muna bukatar a sako fasinjoji sama da 110 na motocin bas guda uku da mahara suka yi garkuwa da su ranar Talata,” wani dan kungiyar, Oumar Ongoiba, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP.
Wani zababben jami’in Bandiagara da ya bukaci a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro ya ce: “Bas din nan uku da fasinjoji sama da 120 na hannun ‘yan tada kayar baya.
'Karuwar hare-haren ta'addanci'
Kungiyoyin Bandiagara, a ranar Juma'a, sun fitar da wata sanarwa inda suka yi Allah wadai da "karuwar hare-haren ta'addanci", da "karuwar mutanen da suka rasa matsugunansu" a garuruwa da kuma "rashin daukar matakin daga rundunar sojin kasar."
Zanga-zangar adawa da rashin tsaro a garin a watan Agustan da ya gabata bayan hare-haren 'yan tada kayar baya ta rikide zuwa tashin hankali inda aka jikkata mutane da dama.
Tun a shekara ta 2012 ne dai kasar ta Mali ke fama da kungiyoyin 'yan tada kayar baya, da dakarun kare kai da kuma 'yan fashi.
Rikicin ya bazu zuwa kasashen Burkina Faso da Nijar da ke makwabtaka da kasar, inda aka yi juyin mulki a dukkan kasashen ukun.
Dabarun sake daidaitawa
Tun bayan hambarar da shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita a watan Agustan shekarar 2020, gwamnatin mulkin sojan kasar ta dauki wani salo mai inganci, tare da wargaza dogon kawancen da ta yi da kasar da ta yi mata mulkin mallaka na Faransa tare da kara kulla alaka ta soji da siyasa da Rasha.
Mali, Burkina Faso da Nijar sun kafa kawancen kasashen yankin Sahel a watan Nuwamba kuma dukkansu sun yi alkawarin ficewa daga kungiyar ECOWAS.
Matsalar tsaro da ke kara tabarbarewa a Mali dai na da nasaba da rikicin jinƙai da na siyasa.
Gwamnatin mulkin sojan dai ta fuskanci suka a cikin gida da waje tun bayan kasa cika alkawuran da ta dauka na gudanar da zaben shugaban kasa a watan Fabrairu sannan kuma ta sauka daga mulki.
Zaɓuka
Firaiminista Choguel Kokalla Maiga ya ce za a gudanar da zabe ne a wannan watan kawai idan har an daidaita matsalar tsaro.
A cewar majiyoyin tsaro da rahotannin kare hakkin bil'adama, tashe-tashen hankula sun ƙaru a tsakiyar kasar Mali a cikin wata uku na karshe na shekarar 2023 lokacin da sojoji suka kara kaimi.
Duk da wannan farmakin, kungiyoyin da ke dauke da makamai na ci gaba da kai hare-hare a tsakiya da kuma kudancin kasar, inda suke zuwa kusa da wajen Bamako babban birnin kasar.
A cikin watan Maris, rundunar sojin kasar ta ce sojojin sun yi artabu da wasu ‘yan ta’adda uku da suka kai wa wani ofishin kwastam mai tazarar kilomita 100 daga Bamako da kuma sansanonin sojoji biyu a kudancin kasar.
Tattaunawar ƙasa
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce ya kasa tantancewa da kansa daga bangarorin biyu daga wurare masu nisa inda ba kasafai ake samun shiga ba. Sojojin Mali ba kasafai suke bayar da rahoton wani farmaki ba, in ban da ikirarin nasara.
A ranar 31 ga Maris, kasa da mako guda bayan da aka shirya mika mulki ga farar hula, jam'iyyun siyasa da kungiyoyin farar hula da dama sun fitar da wata sanarwa da ba kasafai ake samun su ba na neman a yi zabe da wuri-wuri.
Kwanaki bayan haka, an dakatar da duk wasu harkokin siyasa suna jiran sakamakon wata tattaunawa ta kasa da shugaban mulkin soja Kanar Assimi Goita ya kaddamar a watan Disamba.
An kuma haramta yada labaran jam'iyyun siyasa a ƙasar da ke yammacin Afirka.