Mali da Burkina Faso sun tura jiragen yaki Jamhuriyar Nijar ranar Juma'a a wani mataki na nuna goyon baya ga sojojin da suka yi juyin mulki a kasar bayan kungiyar ECOWAS ta bayyana "ranar" da za ta tura dakarunta kasar.
Wani rahoto da aka watsa a gidan talabijin na kasar ya bayyana irin yunkurin hadin gwiwa da Mali da Burkina Faso ke yi na goyon bayan sojojin Nijar da kuma tura jiragen yaki cikin iyakokin kasar.
"Mali da Burkina Faso sun aikata abubuwan da suke fada ta hanyar tura jiragen yaki don yin raddi kan duk wani hari da za a kai wa Nijar," in ji rahoton, yana mai karawa da cewa jiragen yakin da aka tura su ne samfurin Super Tucano.
A taron da suka kammala a Ghana shugabannin tsaron kasashen ECOWAS ba su fadi ranar da dakarunsu za su shiga Nijar ba sai dai sun ce a shirye suke su tafi kasar da zarar an ba su umarnin yin hakan.
Labari mai alaka: Mali da Burkina Faso sun ce za su yaki masu yi wa sojojin Nijar barazana
Kwanakin baya kasashen Burkina Faso da Mali, wadanda ke karkashin mulkin soji, sun fitar da sanarwar goyon baya ga sojojin da suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum sannan suka ce za su dauki duk wani hari da ECOWAS za ta kai wa Nijar tamkar hari ne a kansu.
Mayakan sa-kai
A gefe guda, an soma kafa kungiyoyin mayakan sa-kai na fararen-hula a Nijar domin mayar da martani kan barazanar ECOWAS ta tura dakarunta kasar, a cewar wasu rahotannin kafafen watsa labarai.
Za a soma daukar mayakan sa-kai na kungiyar da aka sanya wa suna Volunteers for the Defense of Niger (VDN) ranar Asabar a Yamai, babban birnin Nijar.
Masu son shiga kungiyar ta VDN za su taru a babban filin wasa na Janar Seyni Kountche inda za a dauki duk wanda yake da shekaru 18 zuwa sama.
Kazalika ana kafa irin wannan kungiya a yankunan da ke kan iyakar Nijar da Nijeriya da kuma Benin.
Kungiyoyin sa-kan za su taimaka wa sojoji ta hanyoyi daban-daban da suka hada da fafatawa a yakin da bayar da gudunmawa a bangaren lafiya da kayan aiki da sauransu.