Zauren Malaman Addinin Musulunci na Nijeriya ya ce yana goyon bayan aurar da ‘yan mata marayu 100 da aka shirya yi a jihar Neja da ke tsakiyar kasar, yana cewa auren ba zai hana 'yan matan karatu ba.
Zauren ya sanar da haka ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma'a, inda ta ce aurar da 'yan matan marayu zai taimaka musu ne wajen tsare mutuncinsu.
Sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da Ministar Mata ta Nijeriya Barista Uju Kennedy Ohanenye take cewa ma'aikatarta ta shirya bai wa 'yan matan 100 'sabuwar rayuwa' da mayar da su makaranta da kuma koya musu sana'o’i.
Tun da farko Ministar ta yi zargin cewa matan da za a aurar ba su isa shekarun aure ba inda ta shigar da kara kotu tana neman ta hana kakakin majalisar dokokin jihar Neja, wanda ya dauki nauyin lamarin, aurar da su.
Sai dai sanarwar malaman, wacce shugaban zauren Malam Aminu Inuwa da Sakatare Injiniya Basheer Adamu Aliyu suka sanya wa hannu, ta ce kamata ya yi ministar mata ta Nijeriya ta fahimci mabambantan al'adu na kasar kafin ɗaukar irin wannan mataki.
Ta ce a matsayinsu na Musulmai, mafi yawancin mutane sun yi riƙo da koyarwar addininsu da tanade-tanaden Shari’a.
"Hatta mutanen da ta’addanci ya shafa sun gwammace su kiyaye tsarin aure maimakon shiga harkokin karuwanci da safarar mutane zuwa Turai, kamar yadda wasu ‘yan Nijeriya da ba za su iya jure matsin tattalin arziki ba suke yi," a cewar sanarwar.
Majalisar ta ce abin da shugaban Majalisar Dokokin Jihar Neja ya yi na ɗaukar nauyi aurar da 'yan matan marayu abin a yaba ne, kuma ya yi dukkan abin da ya kamata, don haka ya kamata a jinjina masa.
"Kundin Tsarin Mulkin Niijeriya ya ba da ‘yancin addini ya kuma san da tanade-tanade Shari’a da ya amince da auren mace da namiji,” a cewar sanarwar.
A cewar sanarwar, kamata ya yi ministar ta yi amfani da ofishinta wajen magance laifuka da ake aikatawa kan mata a fadin Nijeriya, maimakon hana shirin aurar da ‘yan mata marayu.
“Waɗannan laifukan sun haɗa da yadda wasu mata da ‘yan ƙungiyoyin asiri suke safarar ‘yan mata zuwa Turai, da gidajen da ake yi wa mata ciki suna haifar yara ana sayarwa a Kudu Maso Gabas, da kuma yadda ake sace yara daga Arewa zuwa Kudu Maso Gabas don a yi miyagun ayyuka da su,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.
A ranar Juma'ar da ta gabata ne su ma limaman masallatan Juma'a na jihar Neja suka sanar da cikakken goyon bayan tallafin da kakakin Majalisar Dokokin ya bayar wajen aurar da 'yan matan marayu, bayan da aka nemi taimakonsa saboda yadda maraici ya hana aurar da su.
A cikin makon da ke ƙarewa ne ministar ma'aikatar mata ta Nijeriya ta shigar da wata ƙara kotu inda ta nemi a dakatar da aurar da 'yan matan 100 da aka shirya yi a jihar ta Neja har sai an yi bincike kan shekarunsu da kuma tabbatar da cewa ba auren dole za a yi musu ba, kamar yadda sanarwar ma'aikatar ta bayyana.
Lamarin dai ya janyo ce-ce-ku-ce a Nijeriya da martani daga ɓangarori da dama, har ma daga baya wasu suke cewa ministar ta janye ƙarar da ta shigar bayan wasu sarakuna daga jihar ta Neja sun sa baki.
To sai dai a wata sanarwa da Minitsar ta Mata ta Nijeriya Barista Uju Kennedy Ohanenye ta wallafa a shafinta na X ta bayyana cewa ba ta janye ƙarar ba.
Ta bayyana cewa "bayan sa bakin Etsu Nupe Mai Martaba Alhaji Yahaya Abubakar da kuma ziyarar Sarkin Kontagora Mai Martaba Alh Mohammed Muazu da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Neja Rt. Hon. Abdulmalik Sarkindaji, a yanzu muna nemo hanyoyin da za mu warware wannan taƙƙadama."
"Amma har yanzu umarnin kotu yana nan, ban janye ƙarata ba, har sai mun warware wuraren da suke da ƙura," a cewar sanarwar.
Ta ƙara da cewa daga cikin shirin da take yi wa 'yan matan marayu su 100 na Neja akwai ganawa da su da ɗaukar bayanansu, da mayar da su makaranta, da koya musu sana'o'i da shigar da su cikin shirin ma'aikatar na kasuwancin zamani ta hanyar intanet da kuma ba su tallafi.