Miliyoyin mutane ne suka rasa matsugunansu tun bayan soma yakin Sudan. Hoto: AP Archives  

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya ce dakarun sa-kai da ke fafutukar karbe madafun iko a Sudan sun gudanar da kashe-kashen ƙabilanci da ka iya zama laifukan yaki.

Rahoton na Majalisar Dinkin Duniya da kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya rawaito a ranar Alhamis, ya zargi mayakan sa-kai a Sudan da aikata laifuka a yakin neman karbe ikon yammacin Darfur.

Kazalika rahoton ya ba da cikakken bayani kan yadda RSF ta yi nasarar samun ikon hudu daga cikin yankuna biyar na Darfur, ciki har da hanyar hada-hadar kudi wacce ta hada kamfanoni da dama.

Tun a watan Afrilun bara ne Sudan ta fada cikin rudani, bayan shafe tsawon lokaci ana takun saka tsakanin sojojinta karkashin jagorancin Janar Abdel Fattah Burhan, da kuma dakarun rundunar RSF karkashin jagorancin Mohammed Hamdan Dagalo, wadda ta barke kana ta mamaye babban birnin kasar, Khartoum.

Yaduwar rikici

Faɗan ya bazu zuwa wasu sassan kasar, sai dai a yankin Darfur na Sudan, lamarin ya dauki wani salo na daban inda aka yi ta kai hare-hare kan fararen hula, a cewar MDD.

Sai dai mai shigar da ƙara daga kotun ICC Karim Khan, a karshen watan Janairu ya bayyana cewa, akwai wasu dalilai da za su tabbatar da cewa bangarorin biyu na aikata laifukan yaki a Darfur.

Kwamitin kwararru ya ce Darfur na fuskantar "tashe-tashen hankula mafi muni tun daga shekara ta 2005."

Rikicin da ake ci gaba da yi ya haifar da tashi hanakali na jin kai da kuma raba kusan mutane miliyan 6.8 da matsugunansu, yayin da mutane miliyan 5.4 suke tsakanin kasar Sudan sai kuma mutane miliyan 1.4 da suka yi gudun hijira zuwa wasu kasashe, ciki har da kusan mutum 555,000 a makwabciyar kasar Chadi.

Ana zargin duka bangarorin biyu

Dakarun RSF da Sojojin gwamnatin Sudan da ke adawa da juna, duk sun yi amfani da manyan bindigogi da harsasai a wurare da dama da jama'a ke zama, lamarin da ya haddasa barna mai tarin yawa.

"An yi ta kai hare-hare a unguwanni da kan gidaje, kana an yi awon gaba da kayayyaki , sannan an kona da kuma lalata wasu," in ji rahoton.

Rahoton ya jaddada cewa hare-haren wuce gona da iri kan fararen hula - wadanda suka hada da azabtarwa da fyade da kashe-kashe da kuma lalata muhimman ababen more rayuwa na fararen hula - sun zama laifukan yaki karkashin dokar yarjejeniyar Geneva ta 1949.

TRT Afrika