'Yan majalisar dattawan Nijeriya sun yi watsi da bukatar shugaban kasar Bola Tinubu ta neman amincewarsu domin ya tura dakarun kasar Jamhuriyar Nijar.
Sun dauki matakin ne a zaman da suka yi na sirri ranar Asabar.
Sanatocin sun nemi Shugaba Tinubu ya ci gaba da amfani da hanyar lalama wajen shawo kan rikicin da Nijar ta fada a ciki sakamakon juyin mulkin da soji suka yi a makon jiya.
Kazalika sun yi Allah wadai da juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar sannan suka sha alwashin aiki tare da shugaban kasar don ganin an warware matsalar "cikin ruwan sanyi."
Sanata Abdul Ahmed Ningi, ya shaida wa TRT Afirka cewa sun amince a dauki dukkan matakan da suka kamata a kan sojojin Nijar "amma ba za a je yaki da mutanen Nijar ba saboda dangantaka da ke tsakaninta da Nijeriya."
"Mun yi amannar cewa babu wata kasa da take da kusanci da dangantaka da Nijeriya kamar Nijar, don haka Sanatoci da yawa sun yi kalamai masu karfi na hana zuwa yaki," in ji dan majalisar dattawan ta Nijeriya.
A ranar Juma'a ne shugaban Nijeriya ya rubuta wasika ga majalisar dattawan kasar yana neman amincewarta don daukar matakin soji kan dakarun da suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum.
Tun a lokacin 'yan majalisar dattawa na arewacin kasar suka nuna adawarsu game da batun suna masu cewa hakan zai haifar da gagarumar matsala a yankin arewacin kasar wanda jihohinsa bakwai ke da makwabtaka da Jamhuriyar Nijar.
Majalisar ta dauki mataki ne kwana guda kafin wa'adin da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka, ECOWAS ta bai wa sojojin Nijar na mika mulki ga Mohamed Bazoum ke cika.
ECOWAS ta ce ta fitar da wani shiri na sake mayar da hambararren shugaban Nijar Mohamed Bazoum kan mulki.
"An tsara duk wasu shirye-shirye da za su kai ga warware wannan matsala, ciki har da abubuwan da ake bukata da kuma yadda za ta tura dakarun tsaro da lokacin da za mu tura su," a cewar kwamishinan ECOWAS Abdel-Fatau Musah.
"Muna so a samu mafita ta hanyar diflomasiyya, kuma muna so mu aika da wannan sako karara zuwa gare su (sojojin da suka yi juyin mulki) cewa muna ba su kowace dama ta maido da tsarin da suka kifar," in ji shi.
Ranar Juma'a, kasar Chadi da ke makwabtaka da Jamhuriyar Nijar, ta ce ba za ta yi katsalandan a sha'anin kasar ba.