Maikatanga yana ɗaukar hotunan al'adu da kuma rayuwar yau da kullum na mutane. Hoto/Sani Maikatanga

Daga Abdulwasiu Hassan

Sani Mohammed Maikatanga ɗan-jaridar Nijeriya ne mai ɗaukar hotuna wanda son da yake yi wa aikinsa da al'adarsa suka sama masa lambobin yabo daga ɓangarori da dama.

Sani bai bari  talauci ya hana shi ɗaukar hoto ba:Hoto/Sani Maikatanga

A matsayinsa na wanda ya jajirce wajen kiyaye al'adu da kuma rayuwar yau da kullum ta hoto, Maikatanga ya ce ƙalubalen rayuwa bai kashe masa gwiwa wajen gudanar da sana'arsa ba.

Maikatanga yana ɗaukar hotuna ciki har da na  makiyaya da ke yawo  a cikin hamada: Hoto/Sani Maikatanga

Maikatanga, mai kimanin shekara hamsin a duniya, ya lashe gasar ɗaukar hoto uku cikin shekaru biyun da suka wuce.

A shekarar 2022 ya zama gwarzon gasar ɗaukar hoto ta Global landscape Forum Africa wadda ƙungiyar Youths in Landscape Initiatives ta shirya.

Zuwa inda jama'a suka taru a fili: Hoto/Sani Maikatanga

Bayan shekara ɗaya a shekarar 2023, ya lashe kyautar gasar ɗaukar hoto ta Wiki love Africa #Wikiloveafrica (Climate & Weather) da hoton da ya ɗauka na wani mutum da yake ƙoƙarin iyo cikin ruwan da ya yi ambaliya a ƙaramar hukumar Auyo ta jihar Jigawa.

Hotunansa na daukar rayuwar mutane ta yau da kullum. Hoto/Sani Maikatanga

Hoton da ya nuna yadda matsalar yanayi da sare itatuwa da kuma sauyin yanayi ke addabar mutane, ya samu karɓuwa a wajen alƙalan gasar waɗanda suka yi imanin cewa hoton ya tattaro matsalar mutanen da ke fama da ambaliya ke fuskanta.

Fatansu:Photo/Sani Maikatanga

Maikatanga bai tsaya a nan ba, ya ci gaba da ɗaukar hotuna kan batutuwan da suka fi muhimmanci gare shi - al'adu da kuma ƙoƙari na yau da kullum na talakawa.

Ƙoƙarinsa ya sake samun tagomashi yayin da ya lashe kyauta a wata gasar ɗaukar hotuna da aka yi a Afirka ta Kudu.

Sani, wanda ya yi aiki a matsayin ɗan-jarida mai ɗaukar hoto a gidajen jaridu irin su Daily Trust da Leadership, ya ce yana “ƙaunar tafiye-tafiye domin ɗaukar hoton salon rayuwar wurare daban-daban.”

Al'adun kakanni da iyayensu:Hoto/Sani maikatanga

Duk da cewa irin hoton da yake ɗauka na buƙatar kuɗi mai yawa wajen sayen kyamarori da kuma sauran kayan aiki, Maikatanga ya ce yana amfani da kuɗaɗen da yake samu daga gasar ɗaukar hoto domin gudanar da sana'arsa.

Da kuma burinsu: Hoto/Sani Maikatanga

Ya ce yana da burin mallakar kamfanin dillancin hotunan labarai a intanet tare da kafa makarantar koyar da aikin jarida.

TRT Afrika