An kashe mutane da dama a wani hari da aka kai hukumar tsaro ta Chadi ANSE, da ke babban birnin ƙasar N'Djamena, kamar yadda gwamnatin ƙasar ta faɗa a ranar Laraba.
Gwamnatin, wacce ta ɗora alkahin kai harin na cikin dare a kan jam'iyyar hamayya ta ƴan gurguzu ta Socialist Party Without Borders (PSF), wacce Yaya Dillo ke jagoranta, ta ce "a yanzu an shawo kan lamarin baki ɗaya" kuma "an kama waɗanda suka kai harin har ma za a gabatar da su a gaban kotu."
Harin na zuwa ne bayan da aka kama wani jami'in jam'iyyar da zarginsa da "ƙoƙarin kashe shugaban kotun ƙolin ƙasar," in ji gwamnatin.
Dillo babban ɗan adawar shugaban ƙasar gwamnatin riƙon ƙwaryar Chadi Mahamat Idriss Deby Itno ne, kuma ɗan'uwansa ne ta wajen iyayensu.
Zaɓen shugaban ƙasa
Ya ƙaryata batun kai wa shugaban kotun ƙolin yana mai cewa "shiri ne".
Harin da aka kai hukumar ANSE ya faru ne kwana guda bayan sanar da cewa za a yi zaɓen shugaban ƙasa a Chadi ranar 6 ga watan Mayu, wanda ƴan'uwan biyu Mahamat Deby Itno da Dillo suke da niyyar tsayawa takara.
Mahamat Deby ya zama shugaban ƙasar Chadi ne bayan da aka kashe mahaifinsa Idriss Deby Itno a lokacin da suke wani faɗa da ƴan tawaye a shekarar 2021, bayan da ya shafe shekara 30 yana mulkin ƙasar.