Shahararren dan jaridar Peter Magubane ya rasu yana da shekara 91. / Hoto: Reuters

Ana ta gudanar da ta’aziyya ga shahararren mai daukar hoton nan na Afirka ta Kudu Peter Magubane wanda ya rinka daukar hotunan irin zaluncin da aka rinka aikatawa a lokacin nuna wariyar launin fata.

Magubane ya rasu a ranar Litinin yana da shekara 91, kamar yadda kungiyar editoci ta Afirka ta Kudu ta bayyana inda kungiyar ta ce iyalan marigayin ne suka sanar da shi.

Ba a bayyana yadda ya rasu ba, amma kungiyar ta editoci ta ce “ya rasu cikin kwanciyar hankali tare da iyalansa a zagaye da shi.”

An haife shi a Vrededorp da ke wajen Johannesburg - wanda suna wurin a yanzu Pageview - ya kuma girma a Sophiatwon, wanda ya kasance gari ga bakake masu fasaha da aka taba lalatawa sakamakon wariyar launin fata.

An harbe shi sau 17

Farar fata marasa rinjaye a lokacin sun sha kulle Magubane tare da saka masa haramci na shekara biyar wanda ya hana shi aiki ko kuma barin gidansa ba tare da izini ba.

Ya bayyana cewa 'yan sanda farar fata sun taba harbinsa sau 17 da harsashin bindigar shotgun a lokacin da yake aiki.

Magubane ya rasu a ranar 1 ga watan Janairun 2024. / Hoto: Reuters

'Yan sandan sun yi masa duka sannan suka karya masa hancinsa bayan ya ki amincewa ya bayar da hotunan da ya dauka a rikicin Soweto na 1976 bayan dalibai bakaken fata sun yi zanga-zanga kan wata doka wadda ta mayar da harshen Afrikaans tilas a makarantu.

Daya daga cikin hotunansa da suka yi fice akwai wani hoto da ya dauka a wata unguwa ta masu kudi da ke wajen Johannesburg wanda ya nuna wata yarinya farar fata ta zauna bisa wani benci wanda a kansa aka rubata "Turawa kadai" inda wata bakar fata take tsaye kusa da ita tana sharce mata kai

A sakon ta'aziyyar da ta aika, gwamnatin Afirka ta Kudu ta ce Magubane "ya dauki hotunan kusan duka abubuwan tarihi da aka yi na gwagwarmaya da wariyar launin fata."

'Tarihin da ya kafa'

Shugaba Cyril Ramaphosa ya yi ta'aziyya ga iyalan Magubane a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.

"Akasarin rayuwarsa, Peter Magubane ya tattara bayanan tarihi dangane da fafutuka na gwagwarmayar neman 'yanci da kuma cikakkiyar rayuwa a kasarmu," in ji Ramaphosa.

Peter Magubane ya ajiye tairihi ta hanyar daukar hotuna a lokacin. / Hoto: AFP

Ministan al'adu Zizi Kodwa ya rubuta cewa: "Afirka ta Kudu ta yi rashin dan gwagwarmayar neman 'yanci, kwararren mai bayar da labari da kemara... Peter Magubane ba tare da rashin tsoro ba ya ajiye rashi adalci a lokacin."

Jam'iyyar ANC mai mulki ta yi jimamin mutuwar Magubane wanda abin da ya gada ya kasance a cikin tarihin 'yan Afirka ta Kudu baki daya.

"Kyamarar Magubane ta dauki hotunan lamura masu daga hankali da kuma ajiye su, da labarai masu muhimmanci dangane da kasarmu," in ji shi.

'Yar Magubane, Fikile ta tuna da shi a matsayin wanda yake kaunar aikinsa.

"Yana matukar son aikinsa, yana dakatar da komai idan ana batun aikinsa," kamar yadda 'yarsa Fikile Magubane ta bayyana.

TRT Afrika