Kamfanin man fetur na Ƙasa a Libya ranar Alhamis ya ce ƙasar ta yi asarar fiye da $120m sakamakon matakin da gwamnatin da ke gabashin ƙasar ta ɗauka na hana haƙar ɗanyen fetur da sayar da shi a kwana uku da suka wuce.
A wata sanarwa da ya fitar, kamfanin man, wanda ke kula da albarkatun mai na ƙasar, ya ce matakin ya sa fetur ɗin da ake haƙowa a ƙasar ya ragu daga ganga 1,279,386 a ranar Litinin (ranar da aka dakatar da haƙar fetur) zuwa ganga 591,024 a ranar Laraba.
Ranar Litinin, gwamnatin da Majalisar Wakilai da ke gabashin ƙasar ta kafa, wadda Osama Hamad yake jagoranta, ta "hana" haƙar ɗanyen mai da fitar da shi domin mayar da martani kan "harin" da aka kai wa Babban Bakin ƙasar da ke da hedkwata a birnin Tripoli, wanda ke ƙarƙashin shugabancin Al-Siddiq Al-Kabir.
A wata sanarwa da ya fitar ta manhajar bidiyo, Hamad ya ce an rufe rijiyoyin man fetur ɗin ne "domin kare kuɗaden al'ummar Libya da baitalmalun da ke Babban Bankin Libya, da kuma kuma kuɗaɗen da ake samu daga sayar da ɗanyen fetur."
Libya tana samun kashi 90 na kuɗin-shigarta daga ɗanyen fetur da ake fitarwa ƙasashen waje, kuma galibin yankunan da ake haƙo fetur ɗin suna ƙarƙashin ikon gwamnatin Hamad, wadda dakarun da ke gabashin ƙasar waɗanda Janar Khalifa Haftar suke goyon baya.
Tun tsakiyar watan Agusta ake tayar da jijiyoyin wuya a Libya sakamakon rikicin da ke da alaƙa da matakin Majalisar Shugaban Ƙasa na cire Al-Kabir daga shugabancin Babban Bankin ƙasar tare da maye gurbinsa da Mohamed Al-Shoukri. Sai dai Majalisar Wakilan Ƙasar da Majalisar Ƙoli sun yi watsi da matakin, suna masu cewa shugabannin da suka ɗauki matakin "haramtattu" ne.
Baya ga rikici a Babban Bankin ƙasar, Libya tana fuskantar wani rikicin na daban wanda ta kwashe shekaru uku tana ciki sakamakon dambarwa tsakanin Gwamnatin Haɗin-Kan Ƙasa da ke ƙarƙashin Abdul Hamid Dbeibeh, wacce ƙasashen duniya suka amince da ita da ke da hedkwata a Tripoli da kuma gwamnatin Hamad da ke da mazauni a birnin Bengazi.