A tsakiyar yankin Kenya ma'abocin ni'ima, kuma a farfajiyar dajin Shakahola mai yalwar tsirrai, wani al'amarin tsattsauran ra'ayi da kuma mutuwar mutane da yawa ya fara kankama ne a shekarar 2019.
A tsawon shekaru Huɗu da suka biyo baya, wani mummunan bala'i mara misaltuwa ya wakana domin ɗaruruwan mabiya majami'ar Good News International Ministries sun halaka ƙarƙashin jagorancin wani fasto, Nthenge Mackenzie, da aka yi zargin na yaudara ne.
Majami'ar Good News International Ministries, wacce Mackenzie ya assasa a 2003, ta yi wa mabiyanta alƙawarin ceto da ilimin sani Ubangiji.
Faston ya yi amfani da farin jininsa ya tara mabiya masu biyayya cikin sauri, musamman waɗanda ke kuɓuta daga talauci da ƙuncin rayuwa. Koyarwarsa - gaurayen tsattsauran ra'ayi da wahayin tashin duniya - tare da kururuwar waɗanda neman dalilin wanzuwa da kuma abin da ya sa ake rayuwa.
Yayin da ƙarfin faɗa a jin Makenzie ke ƙaruwa, haka ma tasirinsa a kan mabiyansa. Ya cusa tsoro da ra'ayin dogaro da wani a cikin zukatansu, sannu-a-hankali yana katange su daga sauran duniya, sannan kuma yana sake jaddada kansa a matsayin mai iya saka su da hana su shi kaɗai tilo.
Gurguwar fahimta
Koyarwarsa tana ƙara zama ta tsattsauran ra'ayin, yana ba su labarin ƙarewar duniya da kuma buƙatar mabiyansa su shirya wa tafiyarsu aljanna kamar yadda ya musu alƙawari.
A shekarar 2019, Mackenzie ya jagoranci gungun mabiyansa zuwa tsakiyar dajin Shakahola, yana iƙirarin cewa suna kan wata tafiyar ibada ce domin shiryawa ƙarshen duniya. Ya kafa wata cibiya mai faɗin kadada 800 da take jawo hankalin ƙarin jama'a daga Kenya. Amma kuma abin da ya fara a matsayin aikin ibada sai ya rikiɗe cikin sauri ya zama mugun tarko.
Bayyanar bala'i
A ƙarƙashin umurnin Mackenzie, mabiyansa sun ƙaurace wa cin abinci da shan ruwa, suna yi imani da cewa hakan zai tsarkake su kuma ya shirya su domin tafiyarsu ta ƙarshe.
Dayawa, har da ƙananan yara yunwa da ƙishirwa suka galabaitar da su, rayuwarsu ta ƙare da sunan ceto na addini. Ana barin gawarwakin su ruɓe a dajin ko kuma a turbuɗe su a kaburburan da aka haƙa cikin gaggawa.
Masifar ta ƙara ƙazanta ne saboda abin da Mackenzie da masu taya shi suka aikata da gangan: sun hana mabiyansa neman taimako daga wajen ko kuma tserewa daga mummunan yanayin. Su ke sarrafa abinci da ruwa, sun ɓoye wa duniya haƙiƙanin munin lamarin, sannan kuma sun hukunta duk wanda ya ƙalubalance su.
Sai a watan Afrilu 2023 ne, lokacin da wani mutum ya nemi taimakon ƴan sanda wajen nemo matarsa da ƴarsa waɗanda suka tafi Shakahola kafin mahukunta suka gano mummunan lamarin. Gano kaburburan da aka binne mutane da yawa a cikinsu ya girgiza illahirin Kenya, abin da ya haifar da wani gagarumin aikin nemowa da kuɓutar da mutanen.
Gawarwaki 429 aka tono
Cikakken munin bala'in ya ƙara bayyana ne yayin da aka tono ɗaruruwan gawarwaki, abin da ke bayyana sakamakon gurguwar fahimtar Mackenzie. Da aka ritsa shi, ba da jimawa ba sai faston ya miƙa kansa ga ƴan sanda. Matarsa da wasu ƴaƴan ƙungiyar asirin su 16 su ma an tsare su. A watan Mayu, an tuhumi Mackenzie da aikata ta'addaci.
Watanni Huɗu tsakani, an tono gawarwaki 429 daga dajin Shakahola. Ranar 19 ga watan Oktoba, rahoton wani kwamitin majalisar dattawa ta Kenya ya nuna cewa, Mackenzie da ƙungiyarsa, sun tasirantu ne da wata ƙungiyar asiri ta Austaraliya mai suna 'Voice in the Desert'.
Gwamnati na hangen gaba
Matakai na Shari'a a kan Mackenzie da abokan aikinsa na kan gudana, yayin da laifukan da ake tuhumar su da su, suka haɗa da kisan kai, da tunzurawa a kashe kai, da yi wa ƙaramin yaro tsagwaron ƙeta.
An yanke masa hukumcin ɗaurin watanni 18 a gidan yari saboda buɗe sutudiyo da shirya fim ba tare da cikakken lasisi daga Hukumar Tantance Fina-Finai ta Kenya ba.
Gwamnati ta ƙaddamar da bincike kan aikace-aikacen ƙungiyar asirin Mackenzie da kuma ɗaukar matakai don hana afkuwar makamancin haka, hanyar yin ƙoƙarin magance abubuwan da suka jawo bala'in da kuma ƙarfafa dokokin da ke tafiyar da ƙungiyoyin addinai.
An kafa kwamitoci da za su dinga kulawa da mutanen da suka kuɓuta daga Shakahola da iyalansu. Mutane ɗaiɗaiku su ɗari Shida sun ɓata, kuma waɗanda ake zargin su 36 suna tsare a halin da ake ciki.
Tunatarwa ta Gaskiya
Iftila'in da ya bar Kenya da mummunan tabo ya tayar da ƙura game da batun tsattsauran ra'ayin addini, da wasa da hankalin jama'a da ƙungiyar asirin ke yi, da kuma raunin al'ummomin da ake nuna wa wariya.
Har ila yau, ana masa kallon wata tunatarwa ce game da hatsarin bin addini ido rufe da mummunan sakamakon ƙin maganin tsattsauran ra'ayin addini.
Yana kamanceceniya da kashe mutane dayawa a Jonestown da Jim Jones ya yi a Amurka, da kuma kisan dayawa da ƙungiyoyin asiri suka yi a Kunungu da ke Uganda, waɗanda duk biyun suka ba duniya mamaki. Kisan Shakahola wani kukan ƙuruciya ne a kan sa-ido, sannan kuma, wata tunatarwa ce game da muhimmanci tunani mai zurfi da buɗaɗɗiyar zuciya.