Gargadin na UNICEF ya bayyana cewa kusan kananan yara miliyan daya a yankin Sahel na Afirka za su fuskanci matsalar rashin gina jiki a wannan shekara. / Photo: AP

Asusun Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF ya yi gargadin cewa kimanin yara 970,000 ‘yan kasa da shekara biyar a Burkina Faso, da Mali da Nijar za su fuskanci tamowa.

UNICEF ya nemi gwamnatoci da “su sanya batun gina jikin yara kan gaba a manufofin kasa”.

Gargadin na UNICEF ya bayyana cewa kusan kananan yara miliyan daya a yankin Sahel na Afirka za su fuskanci matsalar rashin gina jiki a wannan shekara.

Hakan na zuwa ne a cikin yanayin hauhawar farashin abinci, da rikice-rikice, da kalubalen muhalli.

Wata sanarwar UNICEF ta ranar Juma’a, ta kara da cewa “Ana kiyasin yara 970,000 ‘yan kasa da shekara biyar a kasashe uku na yammacin Afirka da suke yankin Sahel, wato Burkina Faso da Mali da Nijar, za su fuskanci tamowa a wannan shekara”.

Wadannan kasashe uku, Burkina Faso da Mali da Nijar ba su da iyakoki a bakin teku, sannan suna fama da rikice-rikicen ‘yan tayar da kayar baya.

Ana sa ran Nijar ce za ta fuskanci mafi girman matsalar, saboda an kiyasta yara 430,000 za su fada wannan matsalar, wanda ragin kashi 14 ne cikin 100 daga kiyasin 2022. Wannan ragi ya samu ne sakamako yunkurin gwamnatin kasar.

A Mali, an yi hasashen yara 367,000 za su fuskanci matsananciyar tamowa, har sama da kashi 18 cikin 100 daga bara.

Daraktan Gundumar Yammaci da Tsakiyar Afirla a UNICEF, Marie-Pierre Poirier, ta fada a wata sanarwa cewa, “Ta’azzarar rashin tsaro da rikice-rikice yana kara wa yankin hadarin wannan matsala, yayin da kai agaji ga al’ummomi masu nisa yake da matukar wahala.”

Alkaluma na hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya sun nuna cewa karuwar tamowa a yankin Sahel a shekarar 2023 zai hada da wasu yankun kasar Benin, da Burkina Faso da Kamaru da Mali da Mauritaniya da Senegal da Togo.

UNICEF ta yi kira ga gwamnatocin yankin da “su sanya batun gina jikin yara kan gaba a manufofin kasa”.

Kuma su habaka zuba kudi wajen dabarun gano rashin gina jiki da wuri, da kuma yin magani ga yaran da ke fama da tamowa.

TRT World