Fiye da mutum 2,800 ne suka mutu, ciki har da kananan yara, sannan dubbai suka jikkata, a cewar Ma'aikatar Cikin Gida ta kasar./Hoto: Reuters 

Mummunar girgizar kasar da aka yi a Maroko ranar Juma’ar da ta gabata ta shafi yara kimanin 100,000, a cewar Hukumar Kula da Yara ta Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ranar Litinin.

Ko da yake UNICEF ba ta san takamaimai adadin yaran da suka mutu ba da kuma wadanda suka jikkata, sabbin alkaluma daga shekarar 2022 sun nuna cewa yara su ne kashi daya bisa uku na yawan ‘yan kasar Maroko,'' a cewar sanarwar da Hukumar ta fitar.

Girgizar kasar mai karfin maki 6.8 ta shafi yara fiye da 300,000 a Marrakech da yankin Manyan Tsaunukan Atlas, in ji kididdigar Majalisar Dinkin Duniya.

Fiye da mutum 2,800 ne suka mutu, ciki har da kananan yara, sannan dubbai suka jikkata, a cewar Ma'aikatar Cikin Gida ta kasar.

Hukumomi na fargaba adadin yana iya karuwa.

Labari mai alaka: Hotunan girgizar kasar Morocco

Cibiyar Bincike kan Yanayi ta Amurka (USGS) ta ce girgizar kasar ta faru ne da misali karfe 11 na dare a agogon Maroko, kuma ta kai fadin kilomita 75 (mil 46.6) a yankin da birnin Marrakech mai dimbin tarihi yake, yayin da zurfinta ya kai kilomita 18.5.

Girgizar kasar ta yi mummunar illa ga Marrakech, yankin da UNESCO ta ayyana a matsayin wurin tarihi na udniya.

Ranar Litinin masu aikin ceto sun ci gaba da zakulo mutanen da gine-gine suka danne kwana uku bayan aukuwar girgizar kasar.

Ma'aikatan agaji na kasashen duniya da dama sun isa kasar domin taimakawa wurin aikin ceto.

Kawo yanzu Maroko ta amince da taimako daga Sifaniya, Birtaniya, Qatar da Hadaddiyar Daular Larabawa.

Ranar Lahadi, gwamnatin Maroko ta kaddamar da asusun gaggawa a baitul mali da Babban Bankin kasar domin tattara tallafi daga ko ina a duniya.

Girgizar kasar ita ce mafi muni da kasar ta fuskanta a sama da shekaru dari, in ji Cibiyar Nazari kan Yanayin Kasa ta kasar, wato National Geophysical Institute.

AA