Rundunonin sojin Nijar da Burkina Faso sun kashe gomman ‘yan ta’adda a ranar Lahadi a kan iyakokin kasashen, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Burkina Faso ya ruwaito.
Sojojin sun kai samame ne a yankin Goungam da ke cikin Burkina Faso inda jami’an tsaron sama da na kasa suka yi wa ‘yan ta’addan dirar mikiya.
Majiyoyi na soji sun bayyana cewa dakarun sun bayyana cewa runduna ta musamman ta “Phantom” ta Burkina Faso tare da hadin gwiwar sojojin kasa da na sama na kasar da na Nijar sun samu wannan nasarar ne bayan bayanan sirri da suka samu kan ‘yan ta’addan.
Sojojin sun ce a ranar Lahadi 22 ga watan Oktoba ne sojojin Burkina Faso suka hango ‘yan ta’addan a karkashin bishiyoyi a yankin Goungam, daga nan ne jirgin sama ya je ya yi musu luguden wuta.
Haka kuma sojojin sun ce wasu daga cikin ‘yan ta’addan sun mutu sakamakon bama-bamai mallakar ‘yan ta’addan da suka tashi da su.
Sun bayyana cewa bayan luguden wutan sun gano gawarwakin ‘yan ta’addan da yawa da kuma baburansu.
Kamfanin dillancin labaran ya ce sauran ‘yan ta’addan da suka yi saura sun gudu cikin dazukan Nijar inda sojojin saman Nijar din suka kama su.
Kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso na daga cikin kasashen da ke yankin Sahel wadanda suke fuskantar barazana daga ‘yan ta’adda da masu ikirarin jihadi.
Ko a watan da ya gabata sai da kasashen suka kulla yarjejeniyar Liptako Goma wadda yarjejeniya ce ta tsaro domin yaki da ta’addanci.