An sake zaben shugaba Felix Tshisekedi a matsayin shugaban ƙasar Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo DRC a watan Disamba 2023. Hoto: AFP  

Shugaban ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) Moussa Faki Mahamat ya ce yana bibiyar abubuwan da ke faruwa a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC) tare da nuna ''damuwa sosai'' kana ya yi Allah-wadai da yunƙurin juyin mulkin da aka yi a ƙasar.

Rundunar sojin DRC dai ta bayyana cewa a ranar Lahadi ne ta yi nasarar daƙile yunƙurin juyin mulki a kusa da fadar shugaban ƙasar Felix Tshisekedi da ke Kinshasa babban birnin ƙasar lamarin da ake zargin wasu '''yan ƙasashen waje da 'yan Congo ne suka kitsa shi''.

An ji ƙarar harbe-harbe a kusa da Palais de la Nation da ke kusa da fadar shugaban ƙasar a lokacin da aka yi yunƙurin juyin mulkin da safiyar ranar Lahadi, a cewar wasu majiyoyi.

Shugaban ƙungiyar AU Moussa Faki Mahamat, ''ya yi kakkausar suka ga wannan yunƙuri na juyin mulkin, yana mai yaba wa da kuma maraba da sanarwar daƙile lamarin da jami'an tsaron Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo suka yi,'' a cewar sanarwar da ƙungiyar AU ta fitar a yammacin ranar Lahadin.

"Ya yi farin ciki da cewa dukkan shugabannin hukumomin DRC suna cikin ƙoshin lafiya," in ji sanarwar.

"Ya yi amfani da wannan damar wajen yin Allah wadai da yunƙurin kifar da gwamnatin da ma amfani da duk wani ƙarfi don sauya tsarin mulki a kowace ƙasa ta Afirka ta ko wane irin hali ko yanayi."

AFP