Kotun ICC ta taba yanke wa Jean-Pierre Bembe hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekara 10 / Photo: AFP

Shugaban kasar Jamhuriyyar Dimukradiyyar Congo, Felix Tshisekedi ya nada tsohon shugaban kungiyar ‘yan bindiga, Jean-Pierre Bemba a matsayin Ministan Tsaro, biyo bayan wata kwaskwarima da ya yi wa gwamnatinsa.

Wannan ya zo ne yayin da rikice-rikicen ‘yan bindiga ke addabar yankin gabashin kasar.

Kotun kasa da kasa ta ICC ta taba yanke wa Jean-Pierre Bembe, wanda ya taba zama mataimakin shugaban kasa tsakanin 2003 zuwa 2006, hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekara 10.

Amma a shekarar 2018, kotun ta yi watsi da wancan hukuncin. Jean-Pierre Bemba zai maye gurbin ministan tsaro na yanzu, wato Gilbert Kabanda.

Haka nan, an nada tsohon shugaban ma’aikatar fadar Shugaba Tshisekedi, wato Vital Kamerhe a matsayin Ministan Tattalin Arziki.

An taba hukunta shi da laifin almubazzaranci inda aka yanke masa hukuncin shekaru 20 a gidan kaso. Amma daga baya kotu ta wanke shi, sannan ya samu ‘yanci a shekara daya bayan haka.

Mutanen biyu da aka yi wa sabon nadin, ba sa cikin jam’iyyar Shugaba Tshisekedi, mai suna Union of Democracy and Social Progress (UDSP).

Wannan mataki ya zo ne a yayin da kasar ke shirye-shiryen zaben da za a yi a watan Disamba na wannan shekarar, a inda ake kyautata zaton shugaban zai samu sabon wa’adi.

Lokacin sanar da nadin a gidan tabaijin na kasar ranar Alhamis, mai magana da yawun shugaba Tshisekedi ya ce, kwaskwarimar da aka yi wa gwamnatin tana da “alfanu matuka” ga kasar, musamman idan an duba “kwarewar” sabbin ministocin.

TRT Afrika