A watan Agustan da ya gabata ne Yuki Gambaryan, matar Mista Gambaryan ta yi zargin cewa "Rashin lafiyar da yake fama da ita tana ƙara ta'azzara kuma kullum jikinsa na ci gaba da yin tsanani"./Hoto:EFCC

Wata kotun tarayya a Nijeriya ta ƙi bayar da belin babban jami'in Binance, Tigran Gambaryan, wanda ake tsare da shi a ƙasar bisa zarge-zargen da suka haɗa da halasta kuɗin haramun.

Lauyan jami'in na Binance ya shigar da sabuwar buƙata ga alƙalin kotun tarayya da ke Abuja, inda ya nemi a bayar da belin Mista Gambaryan saboda ba shi da ƙoshin lafiya yana mai cewa hakan zai ba shi damar samun kulawa daga ƙwararrun likitoci.

Sai dai alƙalin kotun tarayya, Mai Shari'a Emeka Nwite ya ƙi amincewa da ɓukatar, inda ya ce akwai ƙwararrun likitocin da za su iya kula da lafiyarsa a Nijeriya.

Shari'ar Binance: Gwamnatin Nijeriya ta sha alwashin yin adalci

Alƙalin ya umarci hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Nijeriya ta tura Gambaryan asibiti mai inganci a Abuja tsawon kwana uku zuwa mako biyu tare da rakiyar jami'an tsaro domin a kula da lafiyarsa.

A watan Agustan da ya gabata ne Yuki Gambaryan, matar Mista Gambaryan ta yi zargin cewa "Rashin lafiyar da yake fama da ita tana ƙara ta'azzara kuma kullum jikinsa na ci gaba da yin tsanani".

Ta yi zargin cewa an hana lauyoyi su gana da mijinta tun ranar 26 ga watan Yuli.

Hukumomi a Nijeriya suna tuhumar Binance da jami'ansa guda biyu - Gambaryan, ɗan ƙasar Amurka kuma jami'i kan kiyaye badaƙalar harkokin kuɗi na kamfanin, da Nadeem Anjarwalla, wani ɗan Birtaniya ɗan asalin Kenya wanda shi ne shugaban reshen Afirka na kamfanin da laifin halasta kuɗaɗen haramun da suka kai $35m.

A wata tuhuma ta daban, ana zargin Binance da zille wa biyan haraji a ƙasar.

Binance da Gambaryan sun musanta zarge-zargen. Anjarwalla ya tsere daga gidan yari kuma ya fita daga Nijeriya kafin a soma shari'arsu.

A watan Maris Binance ya ce zai daina duk wata hada-hada da kuɗin Nijeriya sakamakon matakin da gwamnatin ƙasar ta ɗauka na far wa masu harka da kirifto waɗanda ta zarga da hannu a tashin farashin dala a ƙasar lamarin da yake haddasa hauhawar farashin kayayyaki.

TRT Afrika