Abdourahamane Tchiani ya karbi iko da gwamnatin Nijar a ranar 26 ga watan Yulin 2023. Hoto/Others

Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta fitar da sunayen mutum 35 na Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta kasar wato COLDEFF.

An fitar da sunayen ne a ranar Juma’a 3 ga watan Nuwamba kwanaki kadan bayan Shugaban Nijar din Abdourahamane Tchiani ya saka hannu kan dokar da ta kafa hukumar.

Sunayen da aka fitar na mutum 35 sun kunshi sojoji da alkalai da farar hula da sauran jama’a daga bangarori daban-daban.

Sai dai a cikin sunayen, ba a tantance wanda zai kasance shugaba ko mataimaki ko kuma sakataren hukumar ta COLDEFF ba, kamar yadda jaridar ActuNiger ta ruwaito.

Wadanda aka zaba domin zama jami’ai a wannan hukuma sun hada da:

-Lcl Yahaya Moussa Mato

-Cre Lcl Moussa Amadou Kimba

-LClr Abdoulwahid Djibo

-Col Soumana Wali

-Captain Ramatou Zakari

-Lieutenant Illiassou Adaba

-CP Abdourahamane Salah Adoum

-Colonel Habibou Hadiza

-Col/ER Siddo Zakari

-Colonel Zeinabou Moussa Aghali

-Magistrate Issoufou Yacouba

-Magistrate Hassane Madigouh Kanembou

-Me Abder-Rhamane Halidou Abdoulaye

-Me Boubacar Chalaré

-Mr. Abdoul Nasser Oumarou

-Mr. Mai Aiki Boubacar

-Mrs. Issoufou Lady Adamou

-Mr. Garba Halidou Halidou Mahamoud

-Mr. Moumouni Morou

-Mr. Issoufou Kado

-Mr. Elh Sani Bassiri

-Mr. Moumouni Alou

-Mrs. Yacouba Halimatou

-Mr. Abdoua Kabo Ousmane

- Mrs. Djamila Harouna Soungaizé

-Mr Dambadii Son Allah

-Mr. Soll Abdoulaye

-Mrs. Falmate Taya

-Mr. Issa Garba Tahirou

-Mr. Zabeirou Souflanou

-Mr. Haroa Garba

-Mr. Abdourshamane Chalbou Batouré

-Mr. Abdou Idé

-Mr. Moussa Mounkailla Yacouba

-Mr. Mamane Saley Mamane Lawane

Tun bayan hawansa karagar mulki, Shugaban na Nijar Abdourahamane Tchiani ya sha alwashin yaki da cin hanci da rashawa, wanda shi ya sa ma ake ganin dalilinsa na kama wasu daga cikin jami’an tsohuwar gwamnatin Mohamed Bazoum.

Nijar a halin yanzu dai na fuskantar matsaloli daban-daban, daga ciki har da takunkuman da take fuskanta daga kungiyoyin ECOWAS da kuma Tayarrar Turai tun bayan juyin mulkin da ya hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Mohamed Bazoum.

TRT Afrika da abokan hulda