Binance da ke hada-hadar kuɗin kirifto mafi girma a duniya, tana aiki kafaɗa da kafada da hukumomin Nijeriya don warware matsalolin da ke tsakaninsu, a cewar shugaban kamfanin Mista Richard Teng.
Mista Teng ya bayyana haka ne ranar Laraba a Dubai a yayin taro kan kuɗaɗen kirifto mai taken Token2049.
"Abin da zan iya cew shi ne muna aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumomin Nijeriya domin ƙoƙarin ganin mun warware matsalolin da ke tsakaninmu," in ji shi.
Mista Teng ya yi waɗannan kalamai ne a yayin da wata kotu a Nijeriya ta ɗage shari'ar da take yi wa jami'an kamfanin Binance biyu zuwa rnar 2 ga watan Mayu bayan hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya zagon ƙasa, EFCC, ta zarge su da laifuka biyar ciki har da halatta kuɗaɗen haramun da suka kai $34m.
Hukumomi a Nijeriya sun tsare jami'ai biyu na Binance a watan Fabrairu yayin da suka je ƙasar domin tattaunawa da gwamnati kan matakin da ta ɗauka na rufe manhajar.
Sai dai Nadeem Anjarwalla, ɗaya daga cikin jami'an na Binance, ya tsere daga Nijeriya a yayin da yake tsare a hannun hukumomi.
Gwamnati ta ce ta ɗauki matakin ne saboda kamfanın bai yi rajista da hukumomin ƙasar ba, sannan ba ta samun haraji daga ɗimbin ribar da Binance ke samu daga hada-hadar da yake yi a ƙasar, matakin da ke yin illa ga tattalin arzikinta.
Kazalika babu gamsassun bayanai kan adadin ƴan Nijeriya da ke hulɗa da Binance da kuma yawan kuɗin da ake hada-hadar su.
Hasalima, Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, CBN, Olayemi Cardoso, ya ce wasu mutane da ba su sani ba "sun yi hada-hadar dala biliyan 26 ta manhajar Binance a Nijeriya a cikin shekara ɗaya da ta wuce".
Ya ƙara da cewa hakan yana barazana ga tattalin arziki da tsaron Nijeriya.