Nijeriya na fuskantar rashin tsaro musamman a arewacin ƙasar. / Hoto: Reuters

Kotun Tarayyar Nijeriya ta ayyana ƙungiyar Lakurawa a matsayin ƙungiyar 'yan ta'adda, wanda hakan zai bai wa sojojin ƙasar damar amfani da ƙarfi wurin daƙile barazanar da ƙungiyar ke yi a arewa maso yammacin ƙasar.

Alƙali James Omotosho ne ya ayyana ƙungiyar a matsayin ta ta'addanci a wani hukunci da ya yanke a ranar Alhamis, inda ya haramta wa duk wani mutum ko kuma ƙungiya shiga ayyukan ƙungiyar, kamar yadda ofishin Ministan Shari'ar Nijeriya Lateef Fagbemi ya tabbatar a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a.

Tuni dama Nijeriyar ke yakar ƙungiyoyin da ke ɗauke da makamai da dama da suka haɗa da Boko Haram da reshenta na ƙungiyar IS da ke yammacin Afirka da kuma wasu ƙungiyoyin 'yan bindiga da dama.

Ɓullar kungiyar Lakurawa da ta fi tasiri a jihohin Kebbi da Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya, ya kara ta’azzara matsalar rashin tsaro a arewacin ƙasar.

An zargi kungiyar da kai hari a watan Nuwamba a jihar Kebbi wanda ya yi sanadin mutuwar mutane akalla goma sha biyar tare da jikkata wasu da dama bayan sace dabbobi.

Reuters