Kotun Shari’ar Addinin Musulunci a Kano ta yi wa wasu ‘yan daudu bulala goma-goma tare da daurin wata uku-uku a gidan yari ko zabin biyan tarar naira dubu goma.
A wata sanarwa da mai bayar da rahoto kan Hukumar Hisbah a fadar gwamnatin Kano Bashir Muhammad Ahmad ya fitar a ranar Talata, ya ce Kotun Shari’ar Musuluncin ta yanke wannan hukuncin ne saboda ‘yan daudun sun yi shigar mata don yin rawar karya kwankwaso a wajen bikin uban gidansu.
Kotun karkashin jagorancin Mai Shari'a Malam Sani Tamim Sani Hausawa, ta samu matasan 'yan daudun da laifi, bayan an karanto musu tuhumar da ake yi musu, inda nan ta ke suka amsa, sai dai sun roki kotun ta yi musu sassauci.
“Mai Shari'ar ya yanke musu hukuncin daurin watanni uku ko zabin biyan tarar naira dubu goma-goma kowannensu, tare da yi musu bulala goma-goma,” in ji sanarwar.
Mukaddashin kwamandan hukumar Hisbah na jihar Dr. Mujahiddin Aminuddin Abubakar, ya bayyana cewa hukumar ba za ta gajiya ba wajen dakile ayyukan baɗala, domin aikin hukumar shi ne yin hani da aikata mummuna tare da kiran aikata kyakkyawa.