Kotun ECOWAS da ke Abuja babban birnin Nijeriya ta umarci sojojin Nijar su saki hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum nan-take.
Kotun bayar da umarnin ne a zamanta na ranar Juma’a
Kotun ta yi umarni a saki Bazoum "nan-take kuma ba tare da wani sharadi ba" sannan su mayar da shi a kan muƙaminsa.
ECOWAS ta dakatar da Nijar daga cikinta bayan shugaban sojojin da ke tsaron fadar shugaban Nijar ya jagoranci kifar da gwamnatin Bazoum a watan Yuli, sannan sojoji suka tsare shi da iyalansa a gidansa da ke fadar shugaban kasa.
"Mohamed Bazoum shi ne yake wakiltar ƙasar Nijar….shi ne shugaban kasar Jamhuriyar Nijar. An keta dokokin kundin tsarin mulki,” in ji kotun.
Kawo yanzu sojojin ba su mayar da martani game da hukuncin kotun ba. A baya dai, wasu ƙasashe na kungiyar ECOWAS sun yi fatali da umarnin kotun.
A tsakiyar watan Satumba, hambararren shugaban kasar ta Nijar ya gurfanar da sojojin a gaban kotun ECOWAS inda ya buƙaci ta tilasta wa sojojin su sake shi kuma su mayar da tsarin mulki.
"Ba za a iya ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotun ba," a cewar wata sanarwa da lauyoyin Bazoum suka fitar.
A cewar Seydou Diagne, daya daga cikin lauyoyin hambararren shugaban kasar, "a karon farko kotun ta samu sojojin da laifi wadanda suka yi juyin mulki da ya saba wa tsarin mulkin ECOWAS".
"Nauyi ya rataya a wuyan ECOWAS da kasashe mambobinta domin tabbatar da cewa an yi biyayya ga hukuncin kotun," in ji sanarwar lauyoyin.