Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta ba da belin tsohon gwamnan Babban Bankin Nijeriya, CBN, Godwin Emefiele a kan naira miliyan 300 kan sabuwar tuhumar da hukumar EFCC ta shigar a kansa.
EFCC gurfanar da Emefiele ne a gaban kotun a ranar Laraba, kan tuhumarsa da ba da umarnin buga sababbin takardun naira ba bisa ƙa’ida ba, da rashin samun umarni daga fadar Shugaban Ƙasa da kuma sauran shugabannin CBN.
Mai Shari’a MaryAnn Anenih ta karanta masa tuhume-tuhume huɗu da ake masa, ciki har da na ba da umarnin buga sabbin kuɗi da suka kai Naira miliyan 684.5 a kan kuɗi Naira biliyan 18.96.
Emefiele, wanda dama yana fuskantar waɗansu tuhume-tuhumen na almundahana, ya musanta sabbin tuhume-tuhumen.
Lauyansa ya nemi buƙatar kotun ta ba da belinsa bisa alkawarin zai dinga halartar zaman kotun.
Mai Shari’ar ta ba da belinsa a kan Naira miliyan 300 da kuma gabatar da masu tsaya masa har mutum biyu, waɗanda dole su zama ‘yan Nijeriya da suka mallaki gidaje a gundumar Maitama ta Abuja.
Masu shigar da ƙara sun ce daga watan Oktoba 2022 zuwa Maris 2023, Emefiele ya bayar da umarnin buga sabbin takardun kudi ‘yan Naira 1,000, 500 da 200 ba tare da amincewar Shugaban Ƙasa da kuma hukumar CBN ba.
An buga sabbin takardun kudin ne da nufin rage amfani da kudade lakadan “don inganta tattalin arzikin kasar,” amma a maimakon haka sai tsarin ya kawo cikas ga harkokin kasuwanci tare da haifar da wahalhalu ga ‘yan Nijeriya a daidai lokacin da ake shirin gudanar da zaben Shugaban Ƙasa na bara da Bola Tinubu ya lashe.
An kuma tuhumi Emefiele da laifin amincewa da cire kudi naira biliyan 125 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 82.24 daga asusun gwamnati wanda ya saɓa wa dokokin da Majalisar Dokokin Ƙasar ta shimfida.
Tsohon gwamnan Babban Bankin shi ne babban jami’in da ya fuskanci tuhume-tuhumen cin hanci da rashawa a gwamnatin Tinubu.