Firaiministocin uku sun gabatar da jawabi a gaban dubban jama’a da ke murnar ficewar dakarun Faransa daga Jamhuriyar Nijar./Hoto:Reuters

Firaiministocin Nijar da Burkina Faso da Mali ranar Asabar sun jaddada matsayarsu ta samun makoma iri daya karkashin kawancen da ya nesanta su da galibin kasashen Yammacin Afirka tun bayan da aka yi juyin mulki a kasashen.

Sojoji ne suke mulkar kasashen uku bayan da suka kifar da gwamnatocin farar-hula da aka soma a 2020. Hakan ya sanya ba sa jituwa da galibin kasashen kungiyar ECOWAS, wadanda suke kira a gare su da su mika mulki a hannun gwamnatocin dimokuradiyya.

"Daga yanzu, muna cewa, idan kai dan kasar Mali ne ko Nijar ko kuma Burkina, makomarmu daya ce. Za mu kasance tare," a cewar firimiyan Burkina Faso Appolinaire Joachim Kyelem de Tambela a wani taron manema labarai da suka gudanar a Yamai, babban birnin Nijar.

"Makomarmu tana hannayensu," in ji shi.

Kwana guda kafin haka, Firaiministocin uku sun gabatar da jawabi a gaban dubban jama’a da ke murnar ficewar dakarun Faransa daga Jamhuriyar Nijar.

Dukkan kasashen uku sun raba gari da Faransa, wadda ita ce tsohuwar uwar goyonsu, matakin da ya karya tasirin da take da shi a yankin Sahel da kuma yin illa ga yunkurin kasashen duniya na kakkabe masu tayar da kayar baya da ke yankin.

A wani mataki da ke nuna cewa sun samu ‘yanci daga Faransa da ECOWAS, kasashen uku sun yanke shawarar hada gwiwa a fannin tsaro da siyasa da tattalin arziki inda suka kafa kungiyar Kawancen Sahel (AES).

"Mun kafa kungiyar AES. Idan kuka lura, komai ya fara da batun tsaro. A yau, hadin kai tsakanin sojojin kasashen uku ya kai mataki babba. Kuma hakan ya tsorata wasu mutane," in ji Firaiministan Mali Choguel Maiga.

A watan Agusta, cibiyar ACLED ta Amurka wadda ke nazari kan tsaro ta ce bincikenta ya gano an samu karuwar tashe-tashen hankula a Mali da Burkina Faso tun bayan da sojoji suka kwace mulki.

Kasashen ba su yi cikakken bayani game da yadda kawancen nasu zai kasance ba, amma firaiministan Nijar Ali Lamine Zeine ya ce nan gaba duka kasashen za su rika daukar mataki iri daya kan batutuwan da suka shafe su.

Reuters