Mele Kyari ya ce ba shi da wani kamfani ko kasuwanci a ko ina a duniya in ban da wani gidan gona. / Hoto: Mele Kyari

Shugaban kamfanin NNPCL a Nijeriya Mele Kyari ya musanta zargin da shugaban kamfanin Dangote, Aliko Dangote ya yi na cewa wasu ma’aikatan NNPC da ‘yan kasuwa sun kafa injinan gauraya ɗanyen mai a Malta.

Mele Kyari ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X a ranar Talata inda ya ce ya gaji da maganganun da ‘yan uwa da abokan arziki ke yi masa dangane da kalaman na Dangote.

"'Yan'uwa da abokaina sun yi ta kira na game da kalaman da shugaban Kamfanin Dangote ya yi cewa wasu ma'aikatan NNPC sun kafa injinan gwauraya danyen fetur a Malta don kawo tarnaki ga masu samar da fetur na cikin gida.

“Ina so na fayyace cewa, ba na wani kasuwanci kai-tsaye ko ta hanyar dan aike a ko ina a duniya in ban da wani gidan gona. “Kuma ban san wani ma'aikacin NNPC da ya mallaki injinan gwauraya danyen fetur a Malta ko a wata kasa ba,” in ji Mele Kyari.

Shugaban kamfanin na NNPC ya jaddada cewa injin gauraya man fetur a Malta ko kuma wani wuri a duniya ba shi da tasiri kan ayyukan NNPCL.

Ya kuma bayyana cewa kamfanin NNPC zai hukunta duk wani ma’aikacin kamfanin da ya yi hakan hakan kuma ya buƙaci a tona asirin duk wani wanda ya yi hakan ga hukumomin da suka dace domin ɗaukar mataki.

Wannan na zuwa ne yayin da aka shafe sama da mako guda ana samun musayar kalamai da wasu jami’an gwamnatin Nijeriya da shugaban kamfanin Dangote kan batun makamashin man fetur.

Dangoten ya yi zargin cewa akwai masu yi wa matara mansa kafar ungulu, zargin da NNPC da wasu jami’an gwamnatin ƙasar suka musanta.

TRT Afrika