Matatar mai ta Dangote na ta ƙoƙarin samun mai daga kamfanomin da ke haƙo sa. / Hoto: Reuters

Kamfanin mai na Dangote a Nijeriya ya yi kira ga hukumomin Nijeriya da su tursasa wa kamfanonin da ke haƙo mai a Nijeriya su bi dokar man fetur ta Nijeriya wadda ta buƙaci su rinƙa aika wa matatun mai na cikin ƙasar fetur.

Kamfanin na Dangote ya koka kan cewa rashin hakan na ja musu asara.

Matatar man ta Dangote wadda ke iya samar da ganga 650,000 a duk rana wadda shahararren mai kuɗin nan na Afirka Aliko Dangote ya gina a wajen Legas kan dala biliyan 20, na ta gwagwarmaya wurin ganin ta samu isashen mai daga Nijeriya.

A wata sanarwa da matatar man ta Dangote ta fitar a ranar Juma'a, ta zargi hukumar da ke sa ido kan bin dokokin harkokin man fetur ta Nijeriya NURPC da gazawa wurin aiwatar da dokokin samar da ɗanyen mai ga matatun cikin gida.

Abin da ake zato a Satumba

"Damuwarmu a kullum ita ce NUPRC na ta bi, amma kamfanonin mai na ƙasa da ƙasa ba su bin umarni," in ji Anthony Chiejina, wani mai magana da yawun Dangote a wata sanarwa da ya fitar.

"Don haka, sau da yawa muna sayen danyen mai na Nijeriya daga 'yan kasuwa na duniya a kan ƙarin $3- $ 4 a kan kowace ganga wanda ke nufin an samu ƙarin dala miliyan uku zuwa huɗu a kan kowane jirgin ruwa na mai.

Matatar tace tana sa ran za ta karbi jiragen ruwa na mai 15 a watan Satumba wanda a ciki NNPC ta bayar da shida.

TRT Afrika