Daga Kabiru Adamu
Yankin Yammacin Afirka ya tsinci kansa a tsakiyar kokawar karbar iko ko fada a ji tsakanin manyan kasashen duniya.
Babbar alamar hakan ita ce yadda sojoji suke ci gaba da karbe mulki a wasu kasashe a yankin. Duk da cewa yankin ya dukufa wajen tabbatar da tsarin mulkin dimokuradiyya.
A halin da ake ciki, hudu cikin kasashe 15 a yankin: Burkina Faso da Guinea da Mali da kuma Nijar, suna karkashin mulkin soji ne.
Juyin mulkin baya-bayan nan ya faru ne a Nijar a ranar 26 ga watan Yulin shekarar 2023, 'yan makonni bayan Shugaban Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) kuma Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya yi alkawarin jaddada tsarin mulkin dimokuradiyya a yankin.
Gabanin juyin mulkin, an rika nuna kiyayya ga kasar Faransa a Burkina Faso da Guinea da Mali da kuma Nijar. Wani arashi shi ne yadda duka kasashen hudu suka kasance kasashen da Faransa ta yi wa mulkin mallaka.
Babu daga kafa
Batun kin jinin Faransa yana da alaka da yadda ake hako ma'adanai ba tare da 'yan kasashen sun ci moriyar haka ba, ga kuma matsalar tattalin arziki da tsaro.
Saboda wannan kin jinin Faransa da sojojin da suka yi juyin mulkin suka nuna a kasashe hudu, sun samu goyon bayan al'ummar kasashen. Kuma yayin da ake mayar da kasashen saniyar-ware, Rasha da kungiyar sojin haya ta Wagner suna jan su a jiki.
Yayin jawabinsa bayan zamansa Shugaban ECOWAS, Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce kungiyar ba za ta daga kafa ba, ko kawar da idonta wajen kare mulkin dimokuradiyya.
"Wasu masu lura da al'amura sun ce akwai wata sabuwar matsala da ke faruwa a Afirka kuma ta yi kama da tsohuwar matsalar da ta fada wa nahiyar," in ji Shugaba Tinubu.
"Amma, a nan kuma a yanzu, za mu fada wa duk wadanda suke jawo sabuwar matsalar cewa nahiyarmu za ta iya kasancewa tsohuwa, amma zukatanmu sabbi ne. Kuma suna da karfi. Abubuwa marasa dadi da suka faru a baya dole su tsaya a nan. Ba za su kara faruwa ba," kamar yadda ya yi gargadi.
Nauyin da ke wuyan ECOWAS
Shi ya sa ba a yi mamaki ba lokacin da shugabannin kasashe mambobin ECOWAS suka sanar da daukar tsauraran matakai kan Nijar bayan juyin mulkin, wadanda suka hada da amfani da karfin soji idan wa'adin kwana bakwai ya kare (a ranar Lahadi, 6 ga watan Agusta 2023), idan sojojin ba su saki zababben shugaban kasar ba kuma suka mayar da shi kan mulki.
Amfani da karfin soji a Nijar ya yi daidai da matakin ECOWAS na kin yarda da sauyin gwamnatin wanda ya saba wa tanadin kundin tsarin mulkin kasa, kuma kungiyar tana daukar irin wannan matakin ne don mutunta dokarta.
ECOWAS tana da wata ka'ida cewa babu wani dalili da zai sa a amince da sauyin gwamnati a wata kasa, idan hanyar da aka bi ta saba wa kundin tsarin mulki.
Saboda mutunta wannan ka'idar duka mambobin ECOWAS suna da nauyin da ya rataya a wuyansu na mutunta ka'idar a matsayinsu na mambobin kungiyar.
A karshen ganawar tsawon kwana uku da manyan hafsoshin sojin mambobin kasashen ECOWAS, wadanda suka zauna a Abuja daga ranar 3 zuwa 5 ga watan Agustan 2023, Kwamishinan Tsaro da Zaman Lafiya na kungiyar Abdel-Fatau Musah ya ce "an kammala duk wasu shirye-shirye tura dakaru."
Ya ci gaba da cewa sun hada da "duk abin da ake bukata, da yadda da kuma lokacin da za mu tura dakarun."
Kungiyar ECOWAS ba ta kore yiwuwar tattaunawar diflomasiyya. "Muna so tattaunawar diflomasiyya ta yi aiki, kuma muna so mu aika wannan sako karara ga jagororin juyin mulkin don mu ba su damar warware abin da suka yi," in ji Musah.
Wannan yana zuwa ne duk da adawa da amfani da karfin soji da galibin 'yan Nijeriya suke yi.
Makwabta
Yayin da duka wannan ke faruwa, jagororin juyin mulkin Nijar sun dauki matakin bijirewa, inda Shugaba Mohamed Bazoum yake ci gaba da kasancewa a tsare da kuma suke ci gaba da yin sabbin nade-nade yayin da suke ci gaba da neman goyon bayan kasashen yankin da ma na ketare.
Da ma dai Aljeriya da Burkina Faso da Chadi da Guinea da kuma Mali sun nuna adawarsu da amfani da karfin soji a kan Nijar.
Yayin da al'amura suke ci gaba da faruwa, akwai fargaba kan tasirin hakan ga yankin ta fuskar magance matsalar tsaro da kuma dorewar dimokradiyya.
Wasu daga cikin matsalolin da za a iya samu sun hada da ficewar Nijar daga kungiyar kasashe ta G-5 Sahel da rundunar hadin gwiwa (da aka kafa a shekarar 2014); da kuma ficewar Nijar da Rundunar Hadin Gwiwa ta Kasashe ta MNJTF wadanda suke yaki da kungiyoyin ta'addanci.
Akwai kuma fargabar cewa Nijar za ta fice daga Yarjejeniyar Accra wato Accra İnitiative (2017) wadda take taimakawa wajen samar da ayyukan tsaro a kan iyakokin kasashe saboda karuwar ayyukan ta'addanci (da matsalolin sauyin yanayi) a yankin.
Wadannan abubuwa za su kara kawo cikas ga yaki da ta'addanci da masu tayar da kayar baya a yankin.
Yayin da kungiyar ECOWAS da ta Tarayyar Afirka (AU) da sauran kasashen duniya suke ci gaba da mayar da Nijar da Guinea da Mali da Burkina Faso saniyar ware, hakan zai sa za a dauki lokaci kafin a koma tafarkin dimokradiyya a kasashen.
Idan aka ci gaba da samun rabuwar kawuna a Yammacin Afirka, ana tsoron kasashen yankin za su kawar da hankalinsu kan magance matsalar tsaro.
Marubucin, Kabiru Adamu, masani ne kan harkokin tsaro wanda yake zaune a Nijeriya.
Togaciya: Ra'ayoyin da marubuciyar ta gabatar ba sa wakiltar ra'ayoyi da manufofin TRT Afrika.