Daga Sylvia Chebet
Issoufou Issa ya shiga tsaka-mai-wuya. Mutumin, mai shekaru 69, na kwance sakamakon kamuwa da cutar maleriya. Hakan na faruwa ne yayin da kasarsa Jamhuriyar Nijar ta fada hannun sojojin da suka yi juyin mulki.
Yana da gidan sayar da abinci a babban birnin Yamai, amma ya kusa durkushewa tun bayan lamarin da ya afku a ranar 26 ga Yuli na kifar da Shugaba Mohamed Bazoum daga kan mulki da Shugaban Tsaron Fadar Shugaban Kasa ya jagoranta.
Kayan shagon Issa na ci gaba da karewa, babu lantarki a gari, sannan babu masu zuwa shagon don sayen abinci.
Mutane da yawa ba su yi tunanin za a yi juyin mulki ba, amma Issa ya yi hasashen hakan na iya faruwa.
Ya shaida wa TRT Afirka cewa "Juyin mulki ba wata matsala ba ce. Wannan ne halin da ake shiga don samun kyakkawan shugabanci.
Dole a samu juyin mulki idan babu adalci, sannan wasu 'yan tsiraru ne ke amfana da arzikin kasa, maimakon dukkan jama'a su amfana."
Kasar ta Yammacin Afirka ta samu rarrabuwar kai. A ranar da sojoji masu tsaron Bazoum suka kifar da shi daga kan mulki, magoya bayansa sun fara zanga-zanga a wajen ginin majalisar dokoki da ke Yamai inda suke neman da a sake shi nan take, daga baya 'yan sanda suka tarwatsa su.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito wani daga cikin masu zanga-zangar na cewa "Mun zo nan don kare dimokuradiyya, mun zo nan don kare jamhuriya, mun zo nan don bayyana goyon bayanmu ga aiki da doka da oda, sannan mu nuna adawa ga duk wani yunkuri na karbar mulki da bakin bindiga.
"Kuri'un jama'a sun yi nasara kuma Shugaba Bazoum aka zaba don yin shekaru biyar. Mutane sun yi tsayin daka don kare shugabansu."
An koyi sabbin darussa
Kwararru kan sha'anin shugabanci da magance rikici sun bayyana wannan juyin mulki na hudu a tarihin Jamhuriyar Nijar da cewa yana da rikitarwa.
Kungiyar ECOWAS ta yi Allah wadai da juyin mulkin, har ma ta yi barazanar amfani da karfin soji don dawo da farar-hula mulki a kasar ta yankin Sahel.
Joseph Ochieno, kwararre kan alakar kasa da kasa, ya bayyana cewa wannan kokari ya yi wuri, yana mai cewa yadda sojojin Nijar suka bijire wa barazanar kungiyar ya isa a dauki izina kan yadda ake jagorancin kungiyar.
Ya ce "Ina ganin amfani da karfin soji abu ne na rashin tsari, wanda yake barazanar kawo rikici. Ya kamata su fara kokarin tattaunawa... Yanzu dai ga masu juyin mulkin suna samun goyon bayan wasu kasashe - Mali a bangaren yamma, Chadi a bangaren Gabas, da kuma Burkina Faso da ke can tsallake.
Shin wannan ne sabon salon yankin Sahel, watakila don mayar da martani ga wasu rikitattun al'amura?
Batutuwan wajen Nijar
Mummunan yanayin da yankin Sahel ke ciki ya shafi batutuwan ta'addanci da talauci, gami da sabon tsarin rarraba Afirka yadda manyan kasashe ke gogayyar samun karfin fada a ji.
Ochieno ya ce "Kasashen da suke da dimbin arziki, da ya hada da man fetur, zinare da Yuraniyom, ana fitar da su amma ba a ganin 'yan Afirka na amfana da arzikin."
"A lokacin da sojoji suka taso da wannan batu, suna kallon maslahar 'yan kasa. Ba abun mamaki ba ne wannan kifar da gwamnati ya samu amincewa."
Kusan kaso 80 na kasar Nijar na cikin sahara, amma a kasan wannan waje akwai dimbin arzikin Yuraniyom.
Wannan sinadari ne mai daraja, kuma mafi muhimmanci a ayyukan samar da Nukiliya. Faransa na samun kusan dukkan makamashinta daga Nukiliya, kusan shekaru 50 kenan tana diban Yuraniyom daga Nijar.
Mai gidan abinci Issa ya bayyana cewa "Muna daya daga kasashen duniya mafi talauci, amma muna fitar da kayayyaki na biliyoyin daloli zuwa kasashen waje. Wannan ba abun da za a yarda da shi ba ne."
Wasu alkaluma da Bankin Duniya ya fitar a 2018 game da talauci sun nuna cewa 'yan kasar Nijar miliyan 26 na fama da talauci.
Talauci tare da dimbin arziki
Irin wannan abu ne Issa yake ganin ya jefa kasar Nijar cikin tsaka mai wuya da rikicin siyasa.
Kafin juyin mulki na karshe, ya ga sauran hudu da aka yi a baya, har da wanda a 1999 aka kashe Shugaba Ibrahim Baré Maïnassara.
A dukkan wadannan misalai, Issa ya tunatar da cewa, babbar matsalar ita ce ta rashin iya shugabanci, wanda abu ne da gwamnatocin farar-hula suke ganin ba wani abu ba ne.
"Idan 'yan siyasarmu za su dauki darasi, za mu iya magance sake afkuwar juyin mulki a Nijar. A koyaushe sojoji sun fi farar-hula iya jagoranci."
Irin wannan bugun kirji da sojoji suke yi ne ya kamata ya sanya damuwa ga tsarin dimokuradiyya, ba wai a yankin Sahel kadai ba, har da dukkan nahiyar, kamar yadda mai nazari kan siyasa Ochieno ya bayyana.
Ya ce "Batu na gaskiya shi ne akwai bukatar shugabannin siyasar Afirka su farka."
Rashawa da mummunan jagoranci
Masana harkokin siyasa sun ce cin hanci da rashin shugabanci nagari ne suka hana kasashen Afirka ci-gaba, tsawon shekaru bayan sun samu mulkin kai.
"Tsarin dimokuradiyya da ya zauna na tsawon shekaru 30 bai amfani talakan Afirka da wani abun a zo a gani ba. Maimakon haka, abun da ya faru shi ne, kusan dukkan shugabannin da suka zo sun aikata cin hanci da rashawa, bayan hawan su kujerar mulki," in ji Ochieno.
Wani babban abun takaici ma shi ne yadda babu alamun kyakkyawan tsarin kula da lafiya da ilimi da kayan more rayuwa, musamman ma a yankin Sahel.
Mutane irin su Issa na jin cewa arzikin kasar ba karewa yake ba, kawai yana fadawa hannun miyagun masu zuba jari da shugabannin kasashen waje ne.
Amma Ochieno na bayyana ra'ayin cewa ya fi alfanu a samu gwamnatin farar hula da za a daidaita da ita wajen warware al'amura maimakon gwamnatin soji, wanda aikinsu shi ne su tsare kasa.
Mulkin farar hula da na soja
Ochieno ya yi gargadin cewa "Babban batun shi ne shin su (Sojojin) na da wani bambanci da farar-hular ne da ake zaba? Ba koyaushe ne hakan yake ba."
A nahiyar Afirka, an samu juyin mulki da dama suka yi nasara, idan ban da wasu 'yan tsiraru da kasashe irin su Zambia da Malawi da Bostwana da Tanzania da Senegal da kuma Cape Verde.
Juyin mulki na karshe din na shi ne na takwas da aka yi nasarar yin tun 2020. Chadi da Sudan da Mali da Burkina Faso da Guinea na karkashin mulkin sojoji.
A matsayinta na kasar Sahel da ke karkashin mulkin farar-hula, wannan abu da ya faru a Nijar ya janyo samun wata doguwar igiya ta juyin mulki a yankin Sahel da ta taso daga Guinea da ke gabar Tekun Atlantika a Yammacin Afirka har zuwa Sudan da ke gaba da Tekun maliya.
Wannan na nufin cewa miliyoyin 'yan Afirka, da suka hada da Issa, a yanzu haka na karkashin mulkin soji - wani abu da shugabancin nahiyar ya kamata ya yi nazari a kai.