Juyin mulkin da sojoji suka yi a Jamhuriyar Nijar a shekarar da ta wuce yana iya haddasa ƙaruwar ƴan ci-rani da ke isa Tarayyar Turai, a cewar Kwamishina kan Harkokin Gida ta Turai Ylva Johansson ranar Talata, gabanin ƙuri'ar da za a kaɗa don yin garambawul ga dokokin ci-rani na Turai kafin zaɓe a watan Yuni mai zuwa.
Tuni dai sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar a 2023 suka soke wata doka da ta taimaka wurin hana yin ci-rani daga Yammacin Afirka zuwa Turai. Tarayyar Turai tana neman haɗa gwiwa da ƙasashen Yammacin Afirka domin rage masu ci-rani barkatai zuwa Turai.
"Juyin mulkin da aka yi a Nijar yana matuƙar damuna ... Tabbas hakan zai iya sanyawa sabbin ƴan ci-rani su ci gaba da zuwa (Turai) a cikin yanayi mai hatsarin gaske," in ji Johansson a hira da manema labarai.
Wasu alƙaluma na MDD sun nuna cewa baƙin-haure fiye da 45,500 suka tsallaka zuwa Turai a wannan shekarar ya kawo yanzu. Alƙaluman sun ragu sosai idan aka kwatanta da abin da ya faru a 2015 lokacin da baƙin-haure sama da miliyan ɗaya suka shiga Turai, galibinsu ƴan ƙasar Syria.
Tun daga wancan lokaci ne Tarayyar Turai mai mambobi 27 ta ɗauki matakan rage kwararar ƴan ci-rani daga Gabas ta Tsakiya da Afirka ta hanyar tsaurara matakan tsaro a kan iyakokinta da kuma taƙaita karɓar masu neman mafaka.
A bara ne Tarayyar Turai ta sanya hannu kan wata sabuwar yarjejeniya game da ƴan ci-rani, a yayin da take ci gaba da fuskantar matsin lamba daga jam'iyyun ƴan kishin ƙasa waɗanda ake sa rai za su yi nasara a zaɓen Majalisar Dokokin Turai a zaɓen da za a yi nan da wata biyu.
Ranar Larabar nan Majalisar Dokokin Tarayyar Turai za ta kaɗa ƙuri'a ta ƙarshe kan batun ƴan ci-rani, lamarin da zai bayar da dama a age lokacin da ake ɓatawa wurin amincewa da masu neman mafaka, da kuma tsarin komawa da ƴan ci-rani ƙasashensu tare da ba su tallafi.
Idan aka samu amincewar ƴan majalisar kan wannan ƙuri'a, ƙasashen Turai za su sanya mata hannu sannan suna da wa'adin shekara biyu don su aiwatar da ita.
Johansson tana sa rai wannan batu zai samu karɓuwa. Amma ƙungiyoyi 161 na fararen-hula ranar Talata sun yi kira ga mambobin Majalisar Dokokin Turai su yi fatali da ƙudurin, wanda suka ce ya taka ƴancin mutane - ciki har da bayar da dama a tsare ƙananan yara.
"Wannan mataki zai yi tasiri kan ƙananan yaran da ke tsere wa yaƙi da yunwa da kashe-kashen da aka kwashe shekaru ana yi. Yana da matuƙar muhimanci Turai ta guje wa yin kuskure," a cewar Federica Toscano ta ƙungiyar Save the Children Europe.