Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta gayyaci shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasar (NLC), Joe Ajaero, domin amsa tambayoyi game da zargin ɗaukar nauyin ta'addanci da cin amanar ƙasa da laifukan intanet.
Rundunar ta bayyana haka ne a wata takarda da ta aike wa Mr Ajaero ranar Litinin kamar yadda ƙungiyar NLC ta bayyana a shafukanta na intanet.
'Yan sandan sun umarci shugaban ƙungiyar ƙwadagon ya hallara a ofishinsu da ke bincike kan bayanan sirri ranar Talata a Abuja domin amsa tambayoyi, suna masu gargaɗin cewa za a bayar da sammacin kama shi idan ya ƙi bin umarninsu.
Takardar ta ƙara da cewa,“Wannan ofishi yana bincike kan aikata manyan laifuka da ɗaukar nauyin ta'addanci da cin amanar ƙasa da laifukan intanet waɗanda ake zarginka da aikatawa.
“Don haka ana buƙatar ka gabatar da kanka domin amsa tambayoyi ranar Talata, 20 ga watan Agusta, 2024 da misalin ƙarfe goma na safe a Old Abattoir kusa da Guzape Junction, Abuja."
Wannan gayyata na zuwa ne kwanaki bayan jami'an tsaron Nijeriya sun kai samame Hedkwatar NLC da ke Abuja inda suka kwashi wasu takardu da ke da alaƙa da zanga-zangar da aka gudanar a ƙasar kan tsadar rayuwa.
A wancan lokacin, kakakin NLC, Benson Upah, ya fitar da sanarwar da ke cewa ''gomman jami'an tsaro sanye da kayan soja da na gida sun kai hari Labour House inda suka kutsa kai a hawa na biyu da na goma kana suka yi awon-gaba da wasu takardu a cikin motocinsu, suna iƙirarin cewa wai ana amfani da takardun wajen rura wutar zanga-zangar da ake yi Nijeriya.''