Wani harin sama da rundunar sojin sama ta Nijeriya ta kai ya kashe “gomman ‘yan ta’adda” a yayin da suke kokarin tsallaka wani kogi a Jihar Neja, kamar yaddar rundunar sojin ta bayyana.
Jami’an tsaro sun bi sawun ‘yan bindigar daga jihar Zamfara da ke makwabtaka da ita a lokacin da suke kan babura zuwa wani kogi inda suka shiga cikin kwale-kwale, kamar yadda kakakin rundunar sojojin saman Najeriya, Edward Gabkwet ya bayyana a wata sanarwa a ranar Asabar.
“A gefen kogin, ‘yan ta’addan da baburansu 18 sun shiga wani jirgin ruwa mai amfani da inji a yunkurin tsallakawa domin hadewa da sauran ‘yan ta’adda da ke tsallaken kogin. A lokacin ne aka bayar da umarnin bude musu wuta,” in ji shi.
Jami’an tsaron Nijeriya sun shafe sama da shekara goma suna yaki da ‘yan ta’adda irin su Boko Haram da masu garkuwa da mutane a hare-haren sama da kasa.
Masu garkuwa da mutanen na yawan tambayar iyalan wadanda suka kama kudin fansa.
Shugaban ‘yan ta’adda
Hukumomin ba su bayyana takamaimai adadin ‘yan bindigan da suka kashe ba a harin baya-bayan nan da suka kai, sai dai sun bayyana cewa an lalata baburansu 18 da kuma jirgin ruwansu.
Rundunar ta sojin saman ta ce daga cikin ‘yan ta’addan da aka kashe har da wani mai suna Yellow Jambros wanda suka bayyana a matsayin “gawurtaccen dan ta’adda kuma mai garkuwa da mutane”.
Hukumomin sun bayyana cewa Yellow Jambros na da hannu a garkuwa da mutanen da aka rinka yi a kan babban hanya tsakanin Abuja da Kaduna da Neja da Katsina da Zamfara, kamar yadda hukumomin suka tabbatar.
Haka kuma hukumomin sun ce Jambros ya kashe sama da mutum 50 da ya yi garkuwa da su bayan iyalansu sun kasa biyan kudin fansa.
Wani da ake zargin mai garkuwa da mutane mai suna Mohammed Sani, wanda ‘yan sanda suka kama a watan Oktoban 2020 “sakamakon kashe sama da mutane 50 da ya yi saboda rashin iya tattara kudin fansa, ya yi ikirarin cewa yana yi wa Yellow Jambros,” in ji rundunar sojojin saman Najeriya.
Ya kuma yi ikirarin cewa Jambros ya kasance yana samar da kayan aikin soja na bogi da na ‘yan sanda da bindigogi da sauran makamai domin gudanar da ayyukansu.
Motsin da ba a saba gani ba
Mai magana da yawun ‘yan sandan ya ce ba a saba ganin ‘yan ta’adda suna tafiya da tsakar rana da ayarin babura ba.
Wannan harin na baya-bayan nan na zuwa ne kusan mako guda bayan rundunar sojin kasa ta Nijeriya ta kai hari kan masu gudanar da Maulidi bisa kuskure a Tudun Biri da ke Kaduna inda suka kashe akalla mutum 85.
Gabkwet ya bayyana cewa “’yan ta’addan sun yi zaton cewa an dakatar da kai hari ta sama bayan lamari mara dadi da ya faru a Tudun Biri da ke Kaduna inda suka yi kokarin amfani da wannan dama,” in ji Gabkwet.