Wani jirgin soji ɗauke da mataimakin shugaban Malawi Saulos Chilima ya yi ɓatan-dabo a ranar Litinin, kamar yadda gwamnatin ƙasar ta tabbatar.
“Duk wani yunƙuri da hukumomin sufurin sama suka yi domin tuntuɓar jirgin tun bayan ɓacewarsa ya ci tura,” kamar yadda gwamnatin ƙasar ta tabbatar.
Jirgin sojin na Malawi ya ɓata bayan ya bar Lilongwe babban birnin ƙasar a ranar Litinin, kamar yadda sanarwar ta ƙara da cewa.
Shugaban ƙasar ya bayar da umarnin gudanar da bincike tare da gano jirgin bayan da jami’an kula da jiragen suka kasa tuntubar jirgin.
Sanarwar ta ce, tun da farko an shirya saukar jirgin a filin jirgin saman Mzuzu da karfe 10:02 na safe.
Tuni shugaban ƙasar Chakwera wanda zai je kasar Bahamas domin ziyarar aiki, ya soke tafiyar tasa.