Sai dai zuwa yanzu sojojin Mali ba su yi ƙarin bayani a game da wannan harin ba. / Hoto: Reuters

Gwamnatin Mali ta sanar da kashe wani babban kwamandan 'yan tawayen Abzinawa da wasu 'yan tawayen a wani hari da jirgi maras matuƙi a arewacin ƙasar.

Wani ɗan jaridar kamfanin dillancin labarai na Reuters a garin Tinzaouaten da ke kan iyakar Mali da Aljeriya ya shaida harin da aka kai a garin, wanda ke ƙarƙashin ikon wata haɗaka ta ‘yan tawaye wadda ake kira the Permanent Strategic Framework for the Defence of the People of Azawad (CSP-DPA).

“An kashe mayaƙan CSP da dama, ciki har da gawurtaccen nan Fahad Ag Almahmoud,” in ji Chodi Ag, wanda ma’aikaci ne a ma’aikatar watsa labarai ta Mali a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Almahmoud wanda aka fi sani da Gatia, ya kasance tsohon mamba a mayaƙan sa kai da ke goyon bayan gwamnatin Mali, inda daga bisani ya ɓalle ya zama ɗan tawaye a bara.

Wata majiya ta soji wadda ba ta so a faɗi sunanta ta bayyana cewa harin da aka kai a Tinzaouaten ya kashe Almahmoud da wasu “shugabannin ‘yan ta’adda”.

Sai dai zuwa yanzu sojojin Mali ba su yi ƙarin bayani a game da wannan harin ba.

TRT Afrika