Hukumar tattara alkaluma da bayanai ta Tarayyar Nijeriya, NBS ta ce jihar katsina da ke arewa maso yammacin kasar ta kasance daya daga cikin jihohi ukun da man gas na manyan motoci ya fi araha a shekarar 2022.
Alkalluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa jihohi ukun da man ya fi araha sun hada da Bayelsa a kan farashi naira 768.04 da Katsina a kan naira 779.78 da kuma Edo mai farashi naira 797.14.
Jihar Bauchi ce a kan gaba a tsadar man gas din inda aka sayar da man kan kudi naira 910.46 yayin da Abuja ke biye da ita a kan farashi naira 889.44 sai Jihar Adamawa a kan naira 880.33, in ji rahoton da NBS ta fitar.
A fannin gas din girki kuma jihar Kwara ce ke kan gaba wajen tsadar sa inda aka sayar da kilogiram biyar a kan kudi naira 4962.87 yayin da a Abuja aka sayar da shi a kan 4940.00 sai kuma Jihar Adamawa a kan 4915.00.
Rahoton ya ce jihar Kwaran ce ta fi saukin cika tulun gas mai nauyin kilogiram biyar kan kudi naira 4204.45 yayin da jihohin Abia a kan naira 4220.15 da Anambra a kan naira N4232.75 ke bin ta a baya.
Yankin kudu maso gabashin Nijeriya ne ya fi arahar iskar gas na girki inda aka sayar da kilogiram biyar a kan kudi naira 4441.55 yayin da aka sayar da shi a kan naira 4,461,32 a kudu maso kudancin Nijeriya.
A kudu maso yammacin Nijeriya kuwa an sayar da iskar gas kan naira N4,542.52 yayin da aka sayar da shi a arewa maso gabashin Nijeriya kan naira 4,614.67.
Sai arewa maso yammacin Nijeriya inda aka sayar da gas a kan naira 4,651.93 sai kuma aka sayar da shi a kan naira 4,872.20 a arewa maso tsakiyar Nijeriyar.
Layukan waya masu aiki
Yankunan da suka fi yawan layukan waya masu aiki:
- Kudu maso yammacin Nijeriya - 63,541,029
- Arewa maso tsakiyar Nijeriya - 42,616,91
- Arewa maso yammacin Nijeriya - 40,805,145
- Kudu maso kudancin Nijeriya - 32,514,966
- Kudu maso gabashin Nijeriya - 21,548,699
- Arewa maso gabashin kasar - 21,544,848.
Jihohin da ke kan gaba a yawan layukan waya masu aiki:
- Legas - 26,460,867
- Ogun - 12,994,352
- Kano - 12,373,201.
Jihohin da ke kan gaba a karancin layukan waya masu aiki:
- Bayelsa -1,571,692
- Ebonyi - 1,920,996
- Ekiti - 2,001,846.
Bangaren intanet
Jihohin da ke kan gaba wajen yawan layuka masu amfani da intanet:
- Legas - 18,702,394
- Ogun - 9,206,614
- Kano - 8,470,131.
Jihohin da suka fi karancin layuka masu intanet
- Bayelsa 1,101,002
- Ebonyi - 1,264,825
- Ekiti - 1,474,970.
Yankunan da suka fi yawan masu amfani da layuka masu intanet:
- Kudu maso yammacin Nijeriya - 44,787,635
- Arewa maso tsakiyar Nijeriya - 29,609,278
- Arewa maso yammacin Nijeriya - 28,119,575
- Kudu masu kudancin Nijeriya - 22, 506,266
- Arewa maso gabashin Nijeriya -14,994,213
- Yankin kudu maso gabashin Nijeriya - 14,626124.